Indonesia za ta sauya babban birninta saboda Jakarta na nutsewa

Hoton birnin Jakarta. An dauki hoton ranar 5 ga watan Yuli

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kusan rabin birnin a yanzu ya fara nutsewa ta yadda idan teku ya yi ambaliya zai iya shafe shi
An wallafa

Shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo ya sanar da cewa baban birnin kasar zai koma Gabashin Kalimatan kan tsibirn Borneo.

Babban birnin kasar na yanzu Jakarta, wanda fiye da mutum miliyan 10 ke zaune a ciki, na wani yanki mai danshi da tabo ne.

Wasu yankuna na birnin na nutsewa da kusan inchi 10 a duk shekara.

Ba a zabi sunan da za a sanya wa wajen da ake son komawa ba.

Sabon birnin zai kasance tsakanin yankuna biyu da ba su ci gaba ba, Kutai Kertanegara da kuma Penajam Paser Utara.

BBC map
Presentational white space

Za a kashe dala biliyan 32.79 wajen shirin gina sabon birnin, amma cunkoson ababen hawan Jakarta kawai yana lashe tiriliyan 100 na kudin kasar, in ji ministan tattalin arzikin kasar.

Akwai kuma wani babban shiri na rage wa gwamnatin tarayya karfi a shekaru 20 da suka gabata, a wani yunkuri na bai wa jihohi karfi a siyasance da samar musu da hanyoyin samun kudi.

Mafi yawan arzikin kasar yana Jakarta ne, kuma 'yan kasar da dama da ke zaune a Java - tsibirin da Jakarta ke kai - tuni suke korafi kan manta wa da su da aka yi.