Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan kasuwa da 'yan sandan Afirka ta Kudu na gumurzu
An shiga rana ta biyu ta rikicin da ya barke tsakanin bakin haure da 'yan sanda da kuma 'yan Afirka ta Kudu.
An nuna wani bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda wani gini ke ci da wuta a Jeppestown.
'Yan sanda na tuhumar bakin hauren da cinna wa ginin wuta, kuma sun yi gargadin mayar da martani idan 'yan sanda suka ci gaba da kai samame inda suke.
Rikicin ya fara ne ranar Alhamis a lokacin da 'yan sanda suka nemi kai samame cikin yankin hada-hadar kasuwanci da ke tsakiyar birnin na Johannesburg domin kwato kayan da suka ce marasa inganci ne da suke zargin ana sayar wa al'umma.
Amma sai kwatsam 'yan kasuwa, wadanda yawancinsu 'yan kasashen ketare ne suka fara jifan 'yan sandan da duwatsu manya da kanana.
Akwai kuma rahoton da ke cewa wasu 'yan kasashen wajen sun kai hare-hare har sau biyu kan wasu motocin 'yan sanda,
Magajin Garin JoBurg Herman Mashaba ya kai wata ziyara yankin domin ganin irin barnar da aka tafka, kum aya ce tilas ne kowa ya mutunta tsarin doka da oda a birnin.