Abin da ya faru a Afirka a wannan mako

An wallafa

Wasu zabbabun hotuna daga Afirka da 'yan Afirka da ke wasu wuraren na daban cikin makon nan:

Hoton wani zanen tattoo mai siffar nahiyar Afirka jikin kafar wata mata. Tana sanye da takalmin tsini mai kyalkyali.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan hoton zanen tattoo ne na tasawirar nahiyar Afirka jikin kafar wata mata da wani mai daukar hoto ya dauka a lokacin wani taron 'yan kasuwa a Najeriya ranar laraba
Presentational white space
Wata mata lokacin da take wuce wani hoto da ke nuna wata mata mai gashin afro wanda aka zana da fenti.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata mata kenan lokacin da take wuce wani zane a unguwar Maboneng da ke birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu ranar Talata
Presentational white space
Wata yarinya sanye da wata sarkar goshi wanda aka rubuta "fata" a kai lokacin da take ihu. Ya kayatar sosai yadda da take bayyana ra'ayinta.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata yarinya 'yar Kenya yayin da take daga muryarta tare da sauran masu zanga-zanga a inda suke bukatar da a zuba jari kan kulawa da masu cutar daji a ranar Laraba a birnin Nairobi
Presentational white space
Wasu acrobats su biyar a lokacin da suke wasansu a tsaunin Calton Hill da ke Edinburg.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, A cikin shirye-shiryen da ake nunawa a bikin Edinburg Festival Fringe akwai wasu acrobats su biyar 'yan Kenya wadanda aka fi sani da The Black Blues Brothers. A wannan hoton za ku iya ganin yadda suke wasan nasu a Scotland ranar lahadi.
Presentational white space
Damso lokacin da ya rike makirufo kusa da bakinsa yana magana da masu kallonsa. Yana sanye da gilashi da kuma wata riga wacce ke da zane-zane da dama, a bayan sa kuwa akwai zannen mata da aka yi da wuta mai launin shudi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Damso kenan, wani mawaki dan Belgium da kuma Congo a lokacin da yake magana da masu kallonsa a bikin Paleo wanda ya gudana a Switzerland ranar juma'a
Presentational white space
Hoton wata wata mai yin iyo kenan. Ana iya ganin fitillun filin wasan daga cikin ruwan.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata mata 'yar Angola lokacin da take fafatawa a gasar iyo ta duniya wacce aka yi a kudancin Korea
Wasu yara mata kenan su biyar lokacin da suke gab da shukka nasu itacen.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu yara mata kenan su biyar lokacin da suke gab da shuka nasu itace a kasar Habasha wato Ethiopia. Jami'ai da kuma masu taimako a Ethiopia sun shuka miliyoyin itatuwa a ranar litinin. Gwamnati ta ce ta cimma wani matakin da ba a taba cimmawa ba a baya bayan da ta shuka fiye da itatuwa milliyan 350 a cikin kwana daya.
Presentational white space
Wani mutum dan Ethiopia kenan rike da furanni.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu suka sun ce gwamnati na amfani da wannan shirin na shuka itatuwa domin kawar da hankalin mutane daga matsalolin kabilanci da ake fuskanta, wacce ta sanya mutum fiye da milliyan 2.5 suka rasa muhallansu
Presentational white space
Wani jaririn lemur a lokacin da ya makale a cikin mahaifiyarsa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan jaririn lemur ne dan wata daya wanda aka dauki hotonsa a Faransa ranar laraba. Dabbobin lemurs wadanda ake samu a kasar Madagascar na fuskantar barazana a yayin da 1,000 ne kawai suka rage a duniya. Daya daga cikin lemurs din da ke zaune ne a gidajen ajiye namun daji don kallo duk duniya.
Presentational white space
Wani mutum ya sanya hanunnsa kan wuyar wani rakumi. Bakin rakumin dai a bude ya ke kuma yana nuna hakoransa.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mai sayar da rakuma lokacin da yake tsaye da daya daga cikin daruruwan rakuman da yake sayarwa a ranar Laraba a kasuwar Birqash wacce ke kusa da Masar inda ake sayar da rakuma