An sace 'yan Turkiyya hudu a jihar Kwara

An wallafa

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da sace 'yan kasar Turkiyya hudu a Arewa maso Yammacin kasar.

An bayyana cewa mutane hudun da aka yi garkuwa da su ma'aikatan wani kamfani ne na gine-gine kuma an sace su ne a wata mashaya.

'Yan sandan sun bayyana cewa suna kokari wajen ganin cewa sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin yin garkuwa da ma'aikatan.

Ko a makon da ya gabata sai da 'yan fashi a kan teku suka kai hari ga wani jirgin daukar kaya a gabar tekun Najeriya inda suka yi garkuwa da matukan jirgi 10 'yan kasar Turkiyya. Su ma wadannan babu labarinsu.

Matsalar garkuwa da mutane a Najeriya ta zamo ruwan dare inda masu garkuwa da mutane suka fi mayar da hankali wajen garkuwa da masu hannu da shuni a wani lokacin ma har baki 'yan kasar waje.

Ko a watan Afrilun bana, sai da masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da wani babban dan siyasa da diyarsa a hanyar Kaduna kuma ba a sake su ba sai da aka biya kudin fansa.

A dai watan na Afrilun bana, an yi garkuwa da baki 'yan kasar waje har karo biyu.

Da farko an yi garkuwa da wasu manyan ma'aikatan kamfanin mai na Shell a yankin Neja Delta kuma aka kashe 'yan sandan da ke kare rayukansu.

Na biyu kuma ya faru ne a wani wurin yawon bude ido da hutawa a jihar Kaduna inda 'yan bindiga suka kutsa ciki suka kashe wata mata 'yar Birtaniya tare da wani mutum guda sannan suka kuma suka yi garkuwa da mutane uku.

Ko a watan Janairun bana sai da aka yi garkuwa da Amurkawa biyu da kuma 'yan kasar Kanada biyu a hanyar Kaduna zuwa Abuja inda su ma aka kashe 'yan sandan da ke tafe da su.

Sai dai daga baya an samu nasarar ceto su, bayan wani samame da hadin guiwar 'yan sanda da sojoji suka kai, inda suka kwato su da karfi kuma babu wanda ya rasa ransa.