An yi amfani da hoton dungulmin kafar wani ba da izininsa ba

Asalin hoton, Antoine Barège, Radio France
Mutumin mai shekara 60 a duniya dan asalin kasar Faransa ya ce ya kadu matuka a lokacin da ya yi tozali da hoton dungulmin kafarsa a jikin kwalin taba sigari, a matsayin gargadi ga masu shan tabar alhalin babu wanda ya tuntube shi kafin sanya hoton.
An sanya hoton a jikin kwalin tabar tare da gargadi ga masu sha cewa za su iya rasa kafafunsa sanadiyarta.
Sai dai mutumin da ke zaune a Metz ya ce a shekarar 1997 aka harbe shi a kafa a Albania, abin da ya janyo aka yanke kafar.
Lauyansa dai na tuntubar kungiyar Tarayyar Turai dan gano bakin zaren.
Kafar yada labaran Faransa ta rawaito cewa a bara ne dan mutumin ne ya sayo taba sigarin a Luxemburg, sai ya ga hoton kafar wadda ta ke cike da tabo na alamun kuna da ta yi kama da ta mahifinsa.
Ba tare da bata lokaci ba, sai ya zo da kwalin gida dan nuna wa iyayensa.
Kanwarsa ta shaidawa jaridar Le Républicain Lorrain cewa "Dan uwa na ne ya zo da kwalin tabar daga Luxembourg, ba tare da ya ce uffan ba, sai kawai ya ajiye kwalin sigarin a kan teburi."
"Mun kadu matuka, don abu ne da ba mu tsammaci gani ba."
"Dukkan 'yan uwanmu sun ga hoton kafar mahaifinmu ce, kafarsa ce don ga tabon da ke jiki nan na kuna da sauransu."
Mutumin ya ce shi sam bai taba sanin an yi amfani da hoton kafarsa ba. Ya yi amanna an dauki hoton ne a wani karamin asibiti a lokacin da ya je da nufin ganin likatan da zai tabbatar da ko za a iya yi masa kafar katako.
Saboda ya shafe sama da shekara 20 yana amafani da sandar guragu, sakamakon lahanin da harbin da aka yi ma sa na shekarar 1997 a Albania ya haddasa.
'Cin amana'
Lauyan mutumin Antoine Fittante, ya tabbatar da cewa kafar wanda ya ke karewa ce.
"Dukkan tabban da ke jikin kafar hotonsu ne na zahiri a kafarsa, haka kuma dayar kafar mai lafiya ita ma ta na da tabo, kuma ga su nan sun bayyana karara a kwalin tabar.''
"Abin da ban mamaki mutum ya tsinci hotonsa a cikin kwalin taba sigari a matsayin talla ba tare da cimma yarjejeniya da shi ba ake kuma amfani da shi a daukacin kasashen turai," inji lauya Fittente.
"Gaskiya wanda na ke karewa ya muzanta, ya shiga tashin hankali da kaduwa a lokacin da ya ga dungulmin kafarsa ana talla, abin haushin ma har da sako a gefe guda alhalin bai san komai akai ba."
Tuni Mr Fittante ya rubuta wasikar neman bahasi ga asibitin, don sanin wanda ya ba da hoton ba da izinin mai shi ba.
Sannan an tuntubi kungiyar Tarayyar Turai kan batun, saboda alhakin aikawa da hotonan da za a yi amfani da su a irin wadannan abubuwan ya rataya ne a wauyanta.
















