Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Za mu ba Zamfara karin kudi'
Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Honarabul Femi Gbajabiamila, ya yi alkawarin ganin an sama wa jihar Zamfara karin tallafi a kasafin kudin bana, don samun kudin kara gina jihar da samar da ababen more rayuwa da za su inganta rayuwar al'ummar jihar.
Shugaban majalisar ya je jihar ne a wata ziyarar aiki ta yini guda da ya kai domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar kan hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin tsaro da ke kawo tarnaki ga jihar.
A lokacin ziyarar, ya bayar da gudunmawar kayan abinci ga 'yan gudun hijira da abin ya shafa, kuma ya yi alkwarin cewa majalisar tarayya za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin cewa an tallafa wa jihar musamman ta hanyar kasafin kudi domin gudanar da aikin ci gaba da za su farfado da rayuwar jama'a.
Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ya yi alkwarin ba majalisar hadin kai domin ganin cewa an samu saukin matsalolin da ke yankin.
Gwaman ya ce '' Makonni kadan bayan hawan mu karagar mulki, mun fara tattaunawa da 'yan bindiga da kuma 'yansakai.''
''Bayan fara tattaunawar, munyi kokarin kubuto da mutane kusan 113 da aka yi garkuwa da su.''
Ya kuma ce cikin wadanda aka kubutar, mutum biyu 'yan Niger ne 11 kuma daga Sokoto sai daya kuma dan Katsina sauran kuma duk 'yan jihar Zamfara ne.
Jihar ta zamfara ta jima tana fama da matsalar tsaro lamarin da ya kai ga hallaka mutane da yawa da satar da dama domin karbar kudin fansa, lamarin da a baya-bayan nan ya fantsama wasu jihohin makwabtanta irin su Sokoto da Katsina.
Gwamnatin tarayyar Najeriyar ta sha bullo da matakan yaki da wannan matsala ta tsaro a jihar ta Zamfara, amma lamarin kusan ana ganin ya gagara duk da matakan tura sojoji da ake yi.