Rikicin 'yan Shi'a: An tsaurara matakan tsaro a Abuja

An wallafa

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da daukar tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen babban birnin kasar Abuja, tare da gargadin masu tada zaune tsaye su guji fushin hukuma.

A ranar Talata ne aka yi mummunar taho-mu-gama tsakanin mabiya Shi'a da 'yan sanda a majalisar dokokin kasar, inda jami'an tsaro suka yi zargin cewa an harbar musu mutum biyu tare da jikkata wasu shida.

Sufeto Janar na 'yan sanda ya kuma bayar da umarnin zama cikin shirin ko-ta-kwana a dukkan manyan biranen kasar saboda fargabar abin da ka iya faruwa.

To sai dai Muhammad Ibrahim Gamawa daya daga cikin masu magana da yawun 'yan Shi'ar ya musanta zarge-zargen 'yan sandan, inda ya ce ba su da makaman da 'yan sandan suka ce sun yi harbi da su.

Ya kuma kara da cewa sabanin mutum 40 da rundunar 'yan sandan ta ce ta kama musu, an "kama mana kusan mutum 100."

Latsa nan domin sauraron Muhammad Ibrahim Gamawa:

'Yan Shi'ar dai sun ce suna zanga-zanga ne kan ci gaba da tsare jagoransu Sheikh Ibrahim Elzakzaky da gwamnati ke yi wanda suka ya ce "yana cikin mummunan yanayin rashin lafiya".

Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa an kona motoci a harabar majalisar, duk da cewa ba a fayyace wane bangare ne ya yi kone-konen ba.

Lamarin ya janyo an kulle dukkan kofofin shiga harabar majalisar dokokin.

Mabiya Shi'a dai sun dade suna kira da a saki jagoransu wanda hukumomin Najeriya ke tsare da shi tun shekarar 2015.

Irin wannan zanga-zangar ta sha janyo zubar da jini a kasar.