Makwabta sun maka zakara a kotu saboda hayaniya

Asalin hoton, AFP
An fara zaman sauraron wata shari'ah a Faransa kan wani zakara mai suna Maurice bayan wasu tsoffi ma'aurata sun zarge shi da takura musu da yawan cara mai tsananin karfi.
Zakara Maurice wanda cararsa ta asubah ke uzzura wa wasu makwabta, ya ja hankulan jama'a kan karar da kuma shigar da shi gaban kotu a Faransa.
Wasu ma'aurata dattijai ne suka zargi zakaran da gurbata muhalli da hayaniya a wani tsararren tsibirin kasar Faransa na Oléron.
Mai zakaran, Corinne Fesseau, ta ce Maurice na yin abin da aka san duk wani zakara da shi ne.
Zakaran da masu kararsa dai ba su halarci zaman kotun ba a yammacin garin Rochefort ranar Alhamis, don fara sauraron shari'ar.
Sai dai zakaran wanda ya yi fice a tsakanin jama'ar yankin, ya samu goyon baya daga masu zakaru wadanda suka taru a wajen ginin kotu.

Asalin hoton, AFP
Masu karar, Jean-Louis Biron da Joëlle Andrieux, sun gina gidansu na shakatawa ne a kauyen Saint-Pierre-d'Oléron kimanin shekara 15 a baya, daga bisani kuma ya zama gidansu na zaman ritaya.
Daya daga cikin dalilansu na zabar gina gida a yanki, in ji su, shi ne kwanciyar hankalinsu.
Sai dai matsalar Maurice, da kuma abin da suka ce yawan cararsa mai kara ta fara ne a shekarar 2017.
Daga nan sai suka yi wa mai zakaran Ms Fesseau korafi, wadda ke zaune a garin Oléron tsawon shekara 35, lamarin da haifar da rashin jituwa.
Ita dai Ms Fesseau, da magoya bayanta a yankin sun ce batun mai sauki ne - kaji wani bangare ne na rayuwar mutanen karkara, don haka hankali ba zai dauka ba a ce sai an kawo karshen carar da suke yi.
Yanzu dai kotu ta sanya watan Satumba domin sanin irin hukuncin da za ta yanke wa zakara Maurice.









