Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan zanga-zangar adawa da 'yan sintiri a Maiduguri
Masu zanga-zanga sun rufe wata babbar hanya a Maiduguri ranar Lahadi 30 ga watan Yunin 2019 a lokacin wata zanga-zanga da aka yi don kira da a soke kungiyar 'yan sintiri masu yaki da Boko Haram ta CJTF.
Ga wasu hotunan yadda zanga-zangar ta kasance:
Masu zanga-zanga sun rufe wata babbar hanya a Maiduguri ranar 30 ga watan Yunin 2019 a lokacin wata zanga-zanga da aka yi don kira da a soke kungiyar 'yan sintiri masu yaki da Boko Haram ta CJTF.
Masu zanga-zangar dai sun zargi 'yan sintirin da kashe wani direban keke-napep. Sun toshe manyan hanyoyin unguwar Suleimanti tare da kona tayoyi.
Wannan ya janyo rikici duk da kasancewar jami'an tsaro a wurin.
'Yan sintirin na CJTF sun musanta kashe direban da gan-gan, inda suka ce sun harbe shi ne bayan da ya ki tsayawa a duba abun hawansa da daddare a lokacin hana yawo a garin.
Shugaban CJTF na unguwar Suleimanti, Babakura Abba-Ali ya bayyana cewa kin tsayawar da direban ya yi ya sa suka yi tunanin ba shi da gaskiya sai daya daga cikin 'yan sintirin ya harbe shi, saboda suna ganin cewa Boko Haram na yunkurin kai hari a unguwar.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan sintirin sun karfafa sintirinsu da daddare a unguwar a 'yan kwanakin nan bayan wani babban hari da kungiyar Boko Haram ta kai.
'Yan sintirin sun yi kokarin dakatar da zanga-zangar ta hanyar wurga wa masu zanga-zangar sanduna.
An kafa kungiyar sintirin ta CJTF a shekarar 2013 don yaki da Boko Haram a Maiduguri.
An kona tayoyi tare da sa shingaye a wasu titunan unguwar Suleimanti da ke cikin birnin Maiduguri.
Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.