Jirgi ya yi saukar gaggawa kan barazanar tashin bam

An wallafa

Wani jirgin saman kamfanin Indiya na Air India ya yi saukar gaggawa a Landan bayan da wasu bayanan farko suka nuna barazanar tashin bam.

Jirgin mai lamba AI191 ya taso ne daga birnin Mumbai na Indiya zuwa birnin New York na Amurka.

Ma'aikatar tsaro ta ce jiragen yaki na sojin saman Birtaniya RAF sun yi wa wancan jirgin fasinjan rakiya a yayin da yake sauka.

Jirgin Air India ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa barazanar tashin bam ce ta sa jirgin ya sauka, amma daga bisani ya goge sakon, yana mai kiran lamarin da "barazanar tsaro."

Wani sako daga filin jirgin sama na Stansted ya ce jirgin ya sauka ne da misalin karfe 10.15 lokacin Birtaniya, kuma a yanzu haka an kebe jirgin a wani bangare na filin jirgin sama - kuma babu abin da ya samu ainihin wajen saukar.

Filin jirgin saman ya ce ba a san yawan fasinjojin da ke cikin jirgin ba.

Mai magana da yawun RAF ya ce jiragen yakin sun tashi ne daga sansanin RAF na Coningsby da ke gundumar Lincolnshire don raka jirgin Air India zuwa filin jirgin sama na Essex.

Ya ce an ba su izinin yin tsananin gudu kuma yayin da suke wucewa ta kusa da Derbyshire an ji wata kara.

'Yan sanda da masu aikin kashe gobara sun yi ta samun kiraye-kirayen waya daga mutanen da suka ji tsoron ko bam ne ya fashe.

Ma'aikatan agajin ba su iya bayar da wani bayani kan abin da ya jawo karar ba wacce aka ji jim kadan kafin karfe 10 na safe ba, har sai da RAF ta tabbatar da cewa karar injin jirgin yakinsu ne, suka kuma bayar da hakurin tsorata mutane da hakan ya jawo.