Kotu ta daure mawaki AGY saboda cin zarafin Ganduje

An wallafa

Wata kotu a Kano ta yanke wa wani mawaki hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari bayan da ta same shi da laifin bata wa gwamnan jihar suna.

Mawakin Mohammed Yusuf, wanda aka fi sani da AGY, ya yi wata waka mai cike da zambo da habaici, inda ya yi magana kan kirkirar sabbin masarautu a jihar da kuma zargin magudin zabe.

Batun rikicin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi na II da kuma zaben gwamnan da aka yi a watan Maris ya rarraba kawunan 'yan jihar, sannan ya jawo ce-ce-ku-ce a fannoni da dama.

A zaman shari'ar da aka yi ranar Laraba, kotun ta samu Yusuf da laifuka uku da suka shafi yin waka, da sakin bidiyo ba tare da samun amincewar Hukumar tantance fina-finai ta Kano ba, da kuma cin zarafin Gwamna Ganduje.

Rahotanni daga Kano sun ce a ranar Litinin ne aka kama mawakin, sannan aka gurfanar da shi a gaban mai Shari'a Aminu Gabari na kotun majistiri da ke unguwar Noman's Land.

Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin wata shida kan laifi na daya da na biyu ko kuma biyan tarar naira 50,000 kan kowanne, sannan kuma aka yanke masa daurin shekara daya ba tare da zabin biyan tara ba.

Kawo yanzu mawakin bai bayyana matakin da zai dauka ba kan hukuncin.

Wakar, wacce aka yi da manufar koda Sarki Sanusi, na kunshe da zambo ga Gwamna Ganduje.

Ana yawan samun mawaka da ke yin wake-wake inda sukan yi maganganun da suka ga dama kan jama'a musamman shugabannin siyasa, amma ba kasafai akan kai su kotu ba.