Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Har yanzu muna tattaunawa kan batun Sarki Sanusi – Ganduje
Gwamnan jihar Kano ta arewacin Najeriya ya ce har yanzu suna ci gaba da tattaunawa kan rikicin da ya barke tsakaninsa da Sarki Muhammadu Sanusi na II.
Bayan da aka tambaye shi ko har yanzu yana nan kan aniyarsa ta tsige sarkin, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja, ya shaida wa 'yan jarida cewa "har yanzu muna ci gaba da tattaunawa".
Dangantaka ta yi matukar tsami tsakanin bangarorin biyu a baya-bayan nan, abin da ya kai ga gwamnati kirkirar sababbin masarautu, lamarin da kuma yake gaban kotu a yanzu haka.
Yayin da bangaren gwamnati ke zargin Sarkin da tsoma baki a harkokin siyasa, a nasu bangaren, magoya bayansa na zargin gwamnati da kokarin cire shi saboda yana fadar gaskiya da kuma marawa talakawa baya.
Sai dai an samu sa'ida bayan da Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da kuma Alhaji Aliko Dangote suka shiga tsakani inda suka fara yunkurin sasanta shugabannin biyu.
Wannan rikici dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen Kano, kuma ya raba kawunan 'yan jihar da dama.
An samu tashin hankula a sakamakon lamarin, inda har gwamnati da masarautar suka soke wasu daga cikin bukukuwan sallah saboda dalilai na tsaro.
Masu sharhi na ganin zai yi wuya a kawo karshen lamarin a nan kusa, musamman idan aka yi la'akari da yadda bangarorin biyu ke ja da juna, da kuma yadda ake shari'u da dama a gaban kotu.
'Biri bai cinye miliyan bakwai ba'
Gwamna Ganduje ya ce ya je fadar shugaba Buhari ne domin bayyana masa irin matakan da yake dauka na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jiharsa saboda matsalar hare-haren 'yan bindiga da masu satar jama'a da ake fama da shi a Arewa maso Yamma.
"Duk da halin da ake ciki a yankinmu, amma Kano tana daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya saboda matakan da muke dauka," in ji Ganduje.
Sannan kuma ya yi karin haske kan rahotannin da suka ce naira miliyan bakwai sun yi batan-dabo a gidan namun daji na jihar.
Hukumar da Yaki da cin hanci ta Kano ta fara gudanar da bincike kan lamarin, a cewarsa, kuma bayanan farko sun nuna cewa an samu fashi da makami a gidan, amma "ba wai goggon biri ne ya cinye kudin ba kamar yadda wasu masu labaran kanzon-kurege suke yadawa".
"Ba mu da goggon biri ko daya a gidan namun dajin".
Ya kara da cewa "an gaya mana cewa 'yan fashin sun wawure dukkan kudin" da ke cikin akwatin ajiya na gidan zoo din.
Sai dai ya ce akwai alamun cewa an aikata ba daidai ba ko kuma sakaci a wani wurin, amma ya ce bincike ne kawai zai bayyana ainahin abin da ya faru.
Batun batan kudin, wanda na cikin bikin sallah ne da aka yi, ya ja hankalin jama'a sosai inda aka rinka Allah-wadai da shi a shafukan sada zumunta tare da zargin cewa sace su aka yi.