Yadda zane ke kara rura wutar juyin juya hali a Sudan

An wallafa

Masu zane a bango na ci gaba da zane a bangon wuraren da ke kusa da shelkwatar rundunar sojojin Sudan da ke Khartoum a daidai lokacin da dubban 'yan kasar ke ci gaba da zanga-zanga da fafutukar ganin cewa an samu mulkin dimokradiyya.

Muwafaq wanda dalibi ne a wata jami'a da ke kusa da babban birnin kasar na Khartoum ya bayyana cewa wannan zanen da yake yi na nuna yadda mutanen Sudan suka katsa sarkar da ta daure su shekaru da dama.

Da dama daga cikin zanen da ake yi na dauke da sakonni da ke cewa ''harsashi da bama-bamai ba za su yi amfani a yanzu ba''- abin da masu zanga-zangar ke bukata shi ne mika mulki ga gwamnatin farar hula cikin ruwan sanyi.

A yanzu haka masu zanen na kokarin zana hotuna na bai daya masu tsawon kilomita uku da za a shimfida kan hanyar da ake zanga-zangar.

Mughira wani dalibi ne mai koyon fasahar zane inda ya bayyana cewa ya yi wannan zanen a wannan bangon ne domin nuna irin al'adun mutane daban-daban da ake da su a Sudan da kuma suka shiga zanga-zangar.

Kasar na da kabilu da dama da karin harshe daban-daban.

Wannan zane ne a bangon wata jami'a da ke kusa da filin da ake zanga-zangar da ke nuna mutum dauke da wani abin kida da duka kusan kabilun kasar ta Sudan ke amfani da shi.

Wannan na nuni ne da hadin kan 'yan kasar a daidai lokacin da suke bukatar sauyi.

Zanen da ke sama na nuna cewa maza da mata baki daya duka sun bayar da gudummawa wajen fafutukar samun sauyi a kasar.

A nan, wani mai zane ne ke zana Alaa Salah, dalibar nan mai shekaru 22 wacce ta zama tauraruwa a lokacin zanga-zangar inda bidiyonta ya yadu sosai a shafukan sada zumunta.

Akasarin zanen da ake yi ana yin amfani da launukan da suka hada da shudi da rawaya da kuma tsanwa wadanda su ne launukan da ke jikin tutar kasar ta farko tun bayan samun 'yancin kai a 1956.

An daina amfani da tsohuwar tutar a 1970 lokacin mulkin soja inda aka fara amfani da launin da ke jikin tutocin akasarin kasashen larabawa wato launukan fari da baki da tsanwa.

Wannan zanen da ke sama na nufin yadda ake kokarin nuna yadda wasu kasashe ke kokarin dakile juyin yuya halin Sudan.

A cikin zanen, akwai alamar boyayyen hannu wanda hakan na zargin kasashe kamar su Saudi Arabia da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Egypt na goya wa sojoji baya a boye ko kuma ta bayan fage.

Wadannan na cikin mau'du'ai daban-daban da aka yi amfani da su lokacin da aka fara zanga-zangar da suka hada da '' 'yanci da zaman lafiya da kuma adalci.''

Mutane da dama masu fasahar zane na ci gaba da afkawa cikin masu zanen domin bayar da gudummawarsu- hakazalika, an bayyana cewa an ga wasu daga cikin sojoji sun shiga cikin masu zane inda suma suke zanen na su a bango.