Ra'ayoyin jama'a kan kalaman Dangote

Aliko Dangote

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Jama'a da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoiyinsu biyo bayan wasu kalamai da attajirin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote ya yi.

A wata hirarsa da ya yi da Gidauniyar Mo Ibrahim, Dangote ya bayyana cewa ya taba zuwa banki inda ya karbo dala miliyan 10 domin ya tabbatar da cewa da gaske yana da kudi.

Dangote ya bayyana cewa da ya je bankin, ya rubuta takardar karbar kudi sai ya karbi kudin lakadan sa'annan ya zuba su a bayan motarsa.

Amma ya bayyana cewa washe gari ya mayar da kudin zuwa banki domin ci gaba da ajiyarsu.

Tun bayan wannan hira, jama'a da dama na ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan gajeran labarin da attajirin ya bayar.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wannan na bayyana cewa ''gani ya kori ji, wata kila Dangote a da bai yarda yana da irin wadannan kudin ba.''

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wannan kuma na cewa ''me ya sa bai mallaki kulob din Arsenal ba? Wannan ne lokacin da ya kamata ya yi cinikin kulob din.''

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Sai kuma wannan ya ce ''wayyo Allah, ku taimaka ku fada masa cewa kashi daya na kudin nan za su iya sauya rayuwata gaba daya.''

Aliko Dangote wanda dan asalin jihar Kano ne, shi ne wanda ya fi ko wane bakin mutum kudi a duniya kuma babban mai kudin Afirka kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

A kwanakin baya ne dai jaridar ta bayyana cewa arzikinsa ya yi kasa a jerin masu kudin duniya, amma duk da haka ta ce Dangote ne na farko a jerin masu kudin Afirka da sama dala biliyan 10.

Sai dai mujallar Forbes din ta nuna cewa matsalar kasuwa ce da kamfanin siminti na Dangote ya fuskanta ya jawo raguwar arzikin nasa.