'Yan Najeriya na ci gaba da jimamin mutuwar Aisha Lemu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

'Yan Najeriya na cigaba da jimamin rasuwar Hajiya Aisha Lemu, matar shahararren malamin addiinin Musulunci Sheikh Ahmad Lemu.

Hajiya Aisha ta rasu a ranar Asabar din nan tana da shekara 79 da haihuwa bayan ta yi wata gajeruwar jinya.

Babban danta Nurudeen Ahmed Lemu ya fitar da wata sanarwa da ta bayyana cewa ta rasu ne a Minna babban birnin jihar Neja dake arewacin Najeriya.

Sanarwar ta kuma ce za a yijan'izarta a ranar Lahadi da karfe 10 na safe a birnin na Minna.

Cikin wadanda suka mika sakon ta'aziyyarsu ga iyalan marigayiya Aisha Lemu akwai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A wani sakon da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a madadinsa, Shugaba Buhari ya nuna jimaminsa bisa abin da ya kira "Wannan babban rashi da muka yi na kundin ilimi mai muhimmanci wanda ba ya misaltuwa".

Shugaban ya kuma ce: "Aisha Lemu ta yi fice idan aka duba cewa karbar Musulunci tayi daga baya, kuma Baturiya ce, amma ta tashi tsaye domin haskaka duhun jahilci ta hanyar amfani da hasken Musulunci."

Shi ma gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya ziyarci Sheikh Ahmed Lemu a gidansa tare da mataimakinsa domin mika sakon ta'aziyyar al'ummar jihar ta Neja.

Gwamnan ya ce marigayiya Aisha ta kasance mace ta gari kuma abin koyi a fannin addinin Musulunci, wadda kuma ta tsaya bisa tafarkin samar wa mata ilimi domin inganta rayuwarsu:

A shafinsa na Tiwita, Aminu Gamawa ya bayyana ta a matsayin wata fitacciyar malama kuma marubuciya, babbar jagora kuma kwararriyar mai gudanarwa a harkokin addinin Islama.

Ya ce ta taba rike mukamin shugabar makarantar sakandare ta horar da malamai mata a Minna, kuma ita ce ta kafa kungiyar FOMWAN.

Marubuci Gimba Kakanda ma ya bayyana jimaminsa ga wannan rashi.

Ga sakon da ya wallafa a shafinsa na Tiwita:

"A lokacin muna kanana a Minna, litattafan Bridget Aisha Lemu ne muke tunkaho da su, su ne suka fayyace mana batutuwa da dama game da Musulunci, kuma suka sauwwaka mana su. Labarin rayuwarta ma a matsayin baturiyar Ingila da ta karbi Musulunci da kuma karfin imaninta abin koyi ne. Allah Ya gafarta ma ta kurakuranta kuma Ya sanya ta cikin 'yantattun bayinsa."

"Ina mika sanon ta'aziya ga Dr Sheikh Ahmed Lemu, da dan uwa Nurudeen Lemu da 'ya uwa Maryam Lemu da sauran al'umma a ko'ina dangane da rasuwar Hajiya Aisha B Lemu ta IET Minna. Allah ya saka mata da Aljannah Firdaus, Amin. Za a yi janaza da karfe 10 na safiya a Minna...

Wace ce Aisha Lemu?

An haifi marigayiya Bridget Aisha a garin Poole na yankin Dorset na kasar Ingila a 1940.

Tana da shekara 13 da haihuwa sai ta fara tunanin sauya addininta, inda ta fara da duba addinan Hindu da na Bhudda amma basu gamsar da ita ba.

Ta yi karatun jami'a a makarantar koyon al'adu da harsunan kasar Sin da na Afirka a jam'iar Landan (SOAS), inda ta karanta tarihi da al'adu da kuma harshen kasar Sin.

A jami'ar ne kuma ta fara haduwa da dalibai Musulmai wadanda suka rika ba ta litattafan addinin Musulunci, kuma ba da daewa ba sai ta musulunta a shekarar 1961, a lokacin tana shekararta ta farko a jami'a.

A lokacin ne ta bayar da gudunmawarta wajen kafa kungiyar dalibai Musulmai na makarantar ta SOAS a jami'ar Landan, kuma ita ce sakatariyar kungiyar ta farko.

Bayan ta kammala karatun digiri na farko a jami'ar Landan, sai Aisha Lemu ta koma domin karatun babban digiri a kan harshen Ingilishi, kuma a lokacin ne ta fara ganin Sheikh Ahmed Lemu, wanda shi kuma ya isa Landan ne domin karo ilimi a jam'iar ta Landan.

Bayan kammala digirinta na biyu sai ta koma Kano a 1966, inda ta fara koyarwa a makarantar nazarin Larabci, a lokacin shi Sheikh Ahmed Lemu ke shugabancin makarantar.

An daura mata aure da Ahmed Lemu a watan Afrilun 1968, inda Aisha ta kasance matarsa ta biyu.

Ta tafi Sokoto domin kama aiki a matsayin shugabar makarantar mata ta gwamnati.

Daga baya ta koma jihar Neja bayan da aka kirkiri jihar daga cikin jihar Arewa maso yamma ta da a 1976, kuma ta zama shugabar makarantar horar da malamai mata ta Minna har 1978.

Ita da maigidanta sun kafa Gidauniyar Ilimin Islama (IET), kuma ta kafa babbar kungiyar mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) a 1985.

Ta wallafa litattafai na addinin Musulunci

Ta wallafa littafai da dama a fannin addinin Musulunci da ilimi wadanda aka rika amfani da su a makarantun sakandare na Najeriya.

Cikin litattafan da ta wallafa akwai:

  • The Role of Women and Marriage
  • The Ideal Muslim Wife and Husband
  • Animals in Islam
  • Book: The Young Muslim
  • Islamic studies for senior secondary schools
  • Woman in Islam