Tsuntsun da ya je kallon wasan Spaniya

An wallafa

Bisa al'ada, magoya baya ne kan yi dandazo domin mara wa 'yan wasansu baya a duk lokacin da suke buga wasan kwallon kafa.

To amma a wasu lokutan a kan samu wasu halittu da kan kai ziyarar ba-zata a lokacin da wasa ke gudana.

Irin haka ne ya faru a wasan da aka buga tsakanin Spaniya da Iran, a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ke gudana a Rasha.

A wannan lokaci an tsinkayi wani karamin tsuntsu a cikin fili.

'Yan wasan Spaniya biyu ne suka raka tsutsun zuwa gefen fili.

Shahararrun yan wasa, Gerrard Pique da Isco ne suka dauki tsutsun a hankali suka fitar da shi daga cikin filin wasan.

Gerrard Pique, wanda wannan ne karo na 100 da ya buga wa kasarsa Spaniya wasa, ya duka ya dauki tsuntsun da niyyar fitar da shi, amma sai tsuntsun ya tashi daga hannun sa- ya sake dawowa cikin fili.

Daga nan ne shahararren dan wasa Real Madrid, Isco, ya sake daukar tsuntsun a hankali zuwa wajen fili.

Spaniya ce ta yi nasara a wasan da ci daya, Iran kuma aka tashi tana nema.