'Harin Isra'ila ya kashe sama da Falasɗinawa 40 da jikkata gommai'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Aƙalla mutum 40 ne Isra'ila ta kashe tare da jikkata wasu gommai a wadansu hare- hare da ta kai cikin dare a wani sashe da aka ware na ‘yan gudun hijira a kudacin Gaza, in ji rundunar tsaro da kai ɗauki da Hamas ke tafiyarwa.

To amma sojojin Isra’ilar sun ce jiragen samansu na yaƙi sun kai harin ne kan wata cibiya ta mayaƙan Hamas a Khan Younis, kuma ta ɗauki matakan rage yawan farar hula da harin zai rutsa da su.

Mazauna yankin sun sheda wa BBC cewa hare-hare ne guda uku da aka kai kan tantuna da Falasɗinwa ‘yan gudun hijira ke ciki a wajen da aka ware na al-Mawasi, yamma da birnin Khan Younis, abin da ya tayar da wata gagarumar wuta a cikin daren.

Jami’an hukumar ta Falasɗinawa sun ce, harin ya hallaka sama da mutum arba’in da raunata wasu sama da sittin, yayin da wasu ke cikin ɓaraguzai har yanzu.

Waɗanda suka ga lamarin sun sheda wa BBC cewa sun ga wasu manya-manyan fashewa a yankin na al-Mawasi jim kaɗan bayan ƙarfe goma sha biyun dare, inda ake iya ganin wuta na tashi sama.

Wani mai aikin sa-kai da ke zaune kusa da yankin Khaled Mahoud ya ce shi da abokan aikinsa sun garzaya domin su taimaka amma ganin girman wutar lamarin ya ba su tsoro.

An ga wasu hotunan bidiyo da ba a tabbatar da sahihancinsu ba na nuna fararen hula na tona ƙasa da hannunsu domin ceto Falasɗinawa daga katon ramin da bama-baman suka haddasa.

Kakakin sojin Isra’ila ya sanya wani saƙo a shafin Telegram yana cewa sun kai hari kan wata babbar cibiya ta ‘yan ta’addar Hamas, da ya ce suna fakewa a cikin yankin farar hula a Khan Younis.

Sanarwar ta ce kafin harin sun dauki dukkanin matakan da suka wajaba ma rage yawan fara hula da lamarin zai iya shafa, ciki har da amfani da makamai na yankan shakku, da samun ƙarin bayanai na sirri.

Ya ce wannan wani karin misali ne na yadda ƙungiyar ‘yan ta’adda a Zirin Gaza take amfani da kayan farar hula wajen kai hare-hare kan ƙasar Isra’ila da sojojin Isra’ila.

Hamas ta yi watsi da iƙirarin na Isra’ila, cewa da mayaƙanta a wurin, tana mai cewa ƙarya ce tsagwaronta.

Dubban Falasɗinawa ne suka tsere daga yankin na Khan Younis tun bayan da sojojin Isra’ila suka fara kai hare-hare ta ƙasa a watan Oktoba.

Isra’ila na cewa tana kai martani ne na harin ba-zata da Hamas ta kai mata na ranar 7 ga watan Oktoba, wanda a lokacin ta kashe kusan mutum 1200 ta kuma yi garkuwa da 251.

Tun daga sannan Isra’ila ta kashe sama da Falasɗinawa dubu hamsin a Gaza in ji ma’aikatar lafiya da Hamas ke gudanarwa.