Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iran ta yi watsi da kiran ƙasashen Yamma na dakatar da kai wa Isra'ila hari
- Marubuci, David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Iran ta yi watsi da kiraye-kiraye daga Birtaniya da sauran ƙasashen Yamma kan ta haƙura da ramuwar da ta ce za ta yi kan kisan jagoran ƙungiyar Hamas Ismail Haniye a babban birninta Tehran.
Yayin da ake tsaka da kai komo wajen kwantar da hankula, Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya nemi Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya "jingine barazanar kai harin" yayin wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Litinin.
Sai dai Mista Pezeshkian ya ce ramuwar ce "hanyar daƙile aikata laifi" da kuma tabbatar da "yancin Iran", kamar yadda kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ta ruwaito.
Isra'ila, wadda ba ta ce ita ta aikata kisan Haniyeh ba, ta fara shirin ko-ta-kwana na soji.
Amurka ta yi gargaɗin cewa tana shirye-shirye game da "munanan hare-hare" da Iran ko ƙawayenta za su kai a makon nan, kuma har ma ta girka dakarunta a Gabas ta Tsakiya domin taimakawa wajen kare Isra'ila.
Ita ma ƙungiyar Hezbollah mai ƙarfin gaske ta Lebanon ta yi barazanar rama kisan babban kwamandanta a wani hari da Isra'ilar ta kai kan birnin Beirut.
Da yammacin Litinin, shugabannin Birtaniya, da Faransa, da Jamus suka fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa suna shawartar Iran "ta jingine batun kai harin da zai iya ƙara ta'azzara yanayin damuwar da ake ciki a yankin".
"Za su ɗauki alhakin duk matakin da zai jefa 'yar damar da aka samu ta zaman lafiya da tsaro cikin haɗari," a cewar Keir Starmer, da Emmanuel Macron, da kuma Olaf Scholz.
Daga baya firaministan Birtaniya ya sake bayyana damuwarsa kai-tsaye ga shugaban Iran ta waya - karon farko kenan da aka yi irin wannan kiran tun watan Maris na 2021.
Stermer ya faɗa wa Pezeshkian cewa "akwai haɗari mai girma na yin kuskure kuma yanzu ne yakamata a samu kwanciyar hankali da nazari cikin tsanaki", in ji Fadar Downing Street.
"Ya yi kira ga Iran da ta kau da kai daga kai wa Isra'ila hari, yana mai cewa babu wanda ke son yaƙi," a cewarta.
Da safiyar Talata kuma, kamfanin yaɗa labarai na gwamnatin Iran Irna ya ruwaito cewa Mista Pezeshkian ya faɗa wa Stermer goyon bayan da ƙasashen Yamma ke bai wa Isra'ila ne yake saka ta "cigaba da aikata laifuka" da kuma yi wa zaman lafiya da tsaron barazana.
“Pezeshkian ya ce mahangar Iran ta Shari'ar Musulunci, babu wanda ke neman yaƙi a kowane ɓangare na duniya, kuma ya ƙara da cewa hukunta mai tsokana 'yanci ne na kowace ƙasa da kuma hanyar daƙile aikata laifuka da kai hare-hare," kamar yadda Irna ya ruwaito.
Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da kiraye-kirayen: "Babu tunani a wannan shawarar, ta saɓa wa dokokin ƙasashen duniya, ta wuce iyaka," a cewar kakakinta Nasser Kaanani.
Rundunar sojin Isra'ila ta faɗa ranar Litinin cewa tana ɗaukar kalaman na Iran da gaske.
"Muna shirye tsaf wajen kare kai da kuma kai hari, kuma za mu mayar da martani bisa umarnin gwamnati," kamar yadda kakakinta Daniel Hagari ya bayyana yayin wani taro.
Mai magana da yawun fadar tsaron Amurka John Kirby ya faɗa wa manema labarai cewa: "Muna ɗauke da damuwar da ƙawayenmu Isra'ilawa ke da ita game da lokacin [kai hari]. Ƙila a wannan makon ne."
"Abu ne mai wuya a ira ganewa ko Iran za ta kai hari ko kuma ƙawayenta, da irin nau'in harin, amma dai dole ne mu zama cikin shiri," ya ƙara da cewa.
Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya ba da umarnin tura jirgin ruwan yaƙi na biyu mai dakon jiragen sama na yaƙi, da kuma makamai masu linzami na ƙarƙashin ruwa zuwa Gabas ta Tsakiya don abin da ta kira "cikakken shirin Amurka" na kare Isra'ila.