Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool na farautar Isak, Wataƙil Sterling ya je Napoli
Liverpool na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Newcastle da Sweden, Alexander Isak mai shekara 25. (Mail+ - subscription required)
Ita ma Al-Hilal ta Saudiyya na shirin gwada nata sa'ar kan kwantiragin da ake cewa ya kai fam miliyan 130, kan Iska wanda Newcastle ta cire shi daga wasanta na Singapore. (Talksport)
Chelsea da Manchester United sun jingine batun sayo Isak, inda yanzu hankali ya karkata kan ɗan wasan gaba a Brazil, Matheus Cunha mai shekara 26, da kuma ɗan wasan Kamaru, Bryan Mbeumo, mai shekara 25. (Mail)
Newcastle ta mayar da hankalinta kan ɗan wasan Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 22 daga RB Leipzig idan Isak ya tafi. (ipaper)
Aston Villa ta shaida cewa Manchester United cewa ɗan wasanta Ollie Watkins bana sayarwa ba ne, duk da tayin da take samu kan ɗan wasan mai shekara 29 daga Old Trafford. (Telegraph - subscription required)
Leeds United ta amince da yarjejeniya da mai tsaron raga Lyon, Lucas Perri kan £15.6m. (Mail)
Bayern Munich ta shirya gabatar da tayi kan ɗan wasan Liverpool da Colombia, Luis Diaz. (Fabrizio Romano)
Liverpool ta gabatarwa ɗan wasan baya na Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26 sabon kwantiragi domin kawar da tunaninsa daga Real Madrid, nake nuna matsuwa a kansa. (Footmercato - in French)
Ɗan wasan Brazil Douglas Luiz, mai shekara 27, yaƙi halara a rana ta farko da soma atisayen Juventus, yayinda West Ham da Everton da Liverpool kowanne ke nuna zawarcinsu. (Gazetta dello Sport - in Italian)
Ɗan wasan Chelsea Raheem Sterling, mai shekara 30, ya kasance ɗaya daga cikin 'yan wasan da Napoli ke hari. (Calciomercarto - in Italian)
Ɗan wasan Liverpool Harvey Elliott na iya barin Anfield, yayinda yake samun tayi daga West Ham. (Metro)
Spurs na duba yiwuwar gabatar da tayin £15m kan ɗan wasan Koriya ta Kudu, Son Heung-min mai shekara 33. (Sun)
Real Madrid a shirye take ta bada aron ɗan wasanta na gaba mai shekara 19, Endrick saboda kada ta kange makomarsa, amma shi matashin ɗan Brazil ya fi son zama a Bernabeu. (ESPN)