Da gaske ne Isra'ila ta kashe mayaƙan Hamas 10,000? BBC ta yi bincike a kai

A woman cries as she looks at the devastation around her

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Merlyn Thomas & Jake Horton
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • An wallafa

Yayin da rahotanni ke cewa yawan Falasɗinawa da aka kashe a Gaza ya zarce 30,000, Isra'ila na fuskantar matsi kan yawan fararen hula da ake kashewa tare kuma da wani matsin na bayyana shaidun da ke nuna cewa da gaske tana kawar da mayaƙan Hamas kamar yadda ta yi alƙawari bayan harin ranar bakwai ga watan Oktoba.

Sashen BBC mai tantance gaskiyar batutuwa ya duba yawan mayaƙan Hamas da Isra'ila ta kashe.

Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa ta kashe sama da mayaƙan Hamas 10,000 ta hanyar hare-haren da take kaiwa ta sama da kuma samame ta ƙasa a matsayin martani kan harin da Hamas ta kai wanda ya kashe mutanen Isra'ila kimanin 1,200.

Ma'aikatar Dakarun tsaro ta Isra'ila (IDF) a kodayaushe takan kare tsare-tsaren da take amfani da su, inda take nuna cewa tana ƙoƙarin ganin ta kai hari ne a daidai kan mayaƙan Hamas da kuma cibiyoyinsu, tare kuma da rage yawan fararen hula da lamarin zai iya rutsawa da su.

A nata ɓangare ƙungiyar Hamas ba ta fayyace adadin ɓarnar da aka yi wa mayaƙanta ba. To sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahoton cewa wani jamai'in ƙungiyar ya ce mayaƙanta 6,000 ne aka kashe, to amma Hamas ta musanta alƙaluman ga BBC.

Adadin mutanen da suka mutu da ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ke fitarwa, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ke kallo a matsayin na gaskiya, ba ya bambance tsakanin fararen hula da mayaƙan ƙungiyar.

To amma tun fara yaƙin, alƙaluma na nuna cewa aƙalla kashi 70 cikn 100 na waɗanda aka kashe mata ne da ƙananan yara.

Sashen BBC mai tantance gaskiyar batutuwa ya sha tambayar rundunar sojin Isra'ila ta IDF ta yi bayanin hanyoyn da take bi wajen lissafa alƙaluman mayaƙan da suka mutu, to amma rundunar ba ta ce komai ba.

Mun tantance kashe-kashen mayaƙan Hamas ta IDf ta bayyana a sanarwar manema labarai da take fitarwa a shafukanta na sada zumunta.

A ranar 19 ga watan Fabrairu, rundunar IDF ta ce ta kashe mayaƙan Hamas 12,000. Mun tuntuɓi rundunar har sau biyu, amma amsar da muke samu ita ce ''kimanin mayaƙa 10,000'' da kuma ''fiye da 10,000''.

A tsakiyar watan Janairu, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi iƙirarin cewa Isra'ila ta ''lalata'' kashi biyu bisa uku na sansanonin Hamas a Gaza, to sai dai bai bayyana adadin mayaƙan da aka kashe ba.

Kafin fara yaƙin rundunar sojin Isra'ila ta IDF ta ƙiyasta cewa Hamas na da mayaƙa kusan 30,000 a Gaza.

A group of soldiers marching in a parade

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mayaƙan Hamas sun yi fareti a Gaza a 2021, inda rundunar IDF ta ƙiyasta yawan mayaƙan ƙungiyar da kusan 30,000 kafin fara yaƙin
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Disamban bara, Rundunar IDF ta bayyana batun da aka yi na cewa tana kashe fararen hula biyu kafin ta kashe ɗan Hamas guda kamar wata nasara ce kan ƙalubalen da take fuskanta a filin yaƙi.

To amma a ranar 14 ga watan Nuwamba, kusan fiye wata guda da fara yaƙin, IDf ta wallafa a shafinta na Telegram cewa ta kashe '''yan ta'adda 1,000''.

A watan lokacin, ma'aikatar lafiyar ta ce mutum 11,320 ne suka mutu.

Sashen binciken na BBC ya kuma yi nazarin bidiyoyi 280 da rundunar IDF ta wallafa a shafinta na Youtube daga ranar 7 ga watan Oktoba har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.

Sashen ya kuma gano cewa kaɗan ne daga cikin bidiyoyin ke ɗauke da shaidar gani da ido na yawan mayaƙan ƙungiyar da aka kashe.

Daya daga cikin bidiyoyin, da aka wallafa ranar 13 ga watan Disamba - ya nuna gawarwakin mayaƙan. haka kuma akwai wasu bidiyoyi da ke nuna yadda ake harbe mayaƙan.

Mun yi yunƙurin ƙidaya yawan lokutan da dakarun Isra'ila suka yi iƙirarin kashe mayaƙan Hamas a shafin Telegram na IDF.

Mun kuma gano cewa an wallafa bayanai sau 160 na iƙirarin cewa an kashe mayaƙan Hamas, inda adadinsu ya kai 714.

Haka kuma akwai wasu iƙiari har 247 da aka yi amfani da kalmomin ''Masu yawa', ''gommai'' ko ''ɗaruruwa' aka kashe, lamarin da ya bayar da wahala wajen haɗa kan alƙaluman.

Kamar yadda yake da wahala wajen ƙidaya adadin mayaƙan da aka kashe a filin daga. A Gaza, mafi yawan mayaƙan na sanye da tufafin fararen hula ne, kuma sun fi gudanar da ayyukansu a hanyoyn ƙarƙashin ƙasa, sannan mafi yawan kisan da ake yi musu daga hare-hare ta sama ne.

Before and after satellite images show the destruction around the Gazan city of Khan Younis

Tun bayan fara kai hare-haren sojojin Isra'ila zuwa Gaza, rundunar IDF ke zargin Hamas da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa, don samun kariya daga hare-haren Isra'ila.

To amma masana na fargabar cewa Rundunar sojin Isra'ila na ƙidaye fararen hula a matsayin mayaƙan Hamas, saboda suna cikin yankin da ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar.

Andreas Krieg, malami a sashen nazarin tsaro a a jami'ar Kings da ke Landan, ya ce Isar'ila na ɗaukar duka wanda ke yankin da Hamas ke iko da shi a matsayin mamban ƙungiyar, ciki har da ma'aikatan gwamnati da jagororin mulki.

Alƙaluman waɗanda suka mutu da ake samu daga ma'aikatar lafiyar Gaza sun nuna samun ƙaruwar mata da ƙananan yara idan aka kwatanta da yaƙunan baya.

Graphs compare the number of men, women and children killed in this war and previous Gaza conflicts

Wannan "na nuna ƙaruwar fararen hula cikin waɗanda suka mutu," kamar yadda Rachel Taylor, babbar darakta a ƙungiyar da ke ƙidaya waɗanda suka mutu a yaƙi.

Ƙungiyar da ke Birtaniya na aikin tantance adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata a yaƙi.

Kusan rabin mazauna Gaza 'yan ƙasa da shekara 18 ne, kuma kashi 43 na waɗanda suka mutu a yaƙin ƙananan yara ne.

Graph shows the cumulative deaths of men, women and children throughout the current war

"Saɓanin a 2014 inda aka samu adadi mafi yawa na manyan mutane a cikin waɗanda suka mutu, amma a yanzu ba haka abin yake ba,'' in ji ta.

A ƙalla mutum 200 ne ake kashewa a kowace rana tun bayan fara yaƙin, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Gaza ta nuna.

Yawan kashe-kashen da ake yi a yanzu ya ragu idan aka kwatanta da yadda ya fara da farkon rikicin daga watan Oktoba zuwa Disamba.

Amma masana sun shaida wa BBC cewa yawan waɗanda Isra'ila ta kashe na iya ƙaruwa a asibitoci, inda a nan ne ake ƙidaya adadin waɗanda suka mutu, saboda ba sa aiki.

Waɗannan alƙaluma sun ƙunshi na hare-haren soji, banda na yunwa ko wata rashin lafiya, waɗanda ke karuwa kamar yadda ƙungiyoyin agaji suka bayyana.

B'tselem, wata kungiyar kare haƙƙin bil-adama da ke birnin Ƙudus, ta ce yaƙin da ake yi yanzu ya fi laƙume rayukan mutane idan aka kwatanta da rikice-rikicen da suka gabata tsakanin Isra'ila da Gaza.

"Wannan adadi ne da ba mu taɓa ganin irinsa a yaƙunan baya ba da hare-hare a Gaza ko a wasu wurare,'' in ji Dror Sadot mai magana da yawun ƙungiyar.