Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta ragargaji Tottenham gida da waje a Premier a bana
Chelsea ta doke Tottenham 2-0 a kwantan Premier League da suka buga a Stamford Bridge ranar Alhamis.
A minti na 24 da fara wasan ne Chelsea ta zura kwallo a raga ta hannun Trevoh Chalobah daga baya Nicolas Jackson ya kara na biyu, saura minti 18 a tashi daga karawar.
A cikin watan Nuwamba Chelsea ta caskara Tottenham har gida 4-1 a Premier League, har aka bai wa ƴan wasan Tottenham, Cristian Romero da kuma Destiny Udogie jan kati.
Da wannan sakamakon Chelsea tana mataki na takwas a kan teburin Premier da maki 51 da tazarar maki biyu tsakani da Newcastle ta bakwai da tazarar uku tsakani da Manchester United ta shida.
Wannan shi ne karo na 10 da Chelsea ta doke Tottenham gida da waje a kaka daya a Premier League.
Tun kan karawar ta ranar Alhamis wasa daya Chelsea aka ci daga fafatawa 33 a gida da ta fuskanci Tottenham, shi ne 3-1 a Afirilun 2018 karkashin Mauricio Pochettino.
Haka kuma Tottenham ta sha kashi sau 34 a Premier League da ta kara da Chelsea, United ce aka doke sau 39 a hannun Chelsea.
Tottenham ta yi rashin nasara uku daga wasa hudu baya a waje da canjaras daya, wadda a wasa 14 baya ta ci bakwai da canjaras biyar.
Sai dai an ci Chelsea kwallo 59 a Premier League a bana, kakar da aka zura mata kwallaye da yawa a raga a gasar.
An taba zura kwallo 60 a ragar Chelsea a 1991-92, an kuma zura mata 69 a 1990-91 (69).