Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na son daukar Antony da Martinez, Salah ya so tafiya Chelsea
Sabon manajan Manchester United, Erik ten Hag, ya bukaci masu kungiyar su maye gurbin Cristiano Ronaldo da dan wasan Ajax da Brazil, Antony, mai shekara 22, idan suka amince dan wasan gaba na Portugal ya bar kungiyar a kakar wasa ta bana. (Sunday Mirror)
Manchester United na kokarin shan gaban wasu kungiyoyi domin daukar dan wasan Arsenal Lisandro Martinez, tare da yi wa Ajax tayin £38m ga dan wasan baya na Argentina mai shekara, 24. (Mail on Sunday)
Kazalika Arsenal da Manchester United na fadi tashin daukar dan wasan Jamus Serge Gnabry, mai shekara 26, daga Bayern Munich kan £40m. Tsohon dan wasan Gunner zai tafi Bayern a kakar wasa mai zuwa. (Star Sunday)
Gnabry na sahun gaba cikin wadanda Manchester City ke zawarci, idan suka sayar da dan wasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 27, a wannan kakar. (Sunday Sun)
Mohamed Salah ya so tafiya Chelsea gabanin dan wasan gaban na Masar mai shekara 30, ya amince da sabon kwantiragi, wadda ta sanya ya zama mafi tsada a tarihin Liverpool. (Sunday Sun)
Barcelona ba ta da niyyar saida dan wasan tsakiya na Netherlands, Frenkie de Jong, duk da cewa kungiyar Manchester United na fakon dan wasan mai shekara 25, tare da amincewa ta biya makudan kudade. (AS - in Spanish)
Ana sa ran Nicolas Tagliafico zai bar Ajax a kakar wasan bana, yayin da Brighton da Lyon ke sahun gaba a kulob-kulob din da ke nuna sha’awar daukar dan wasan baya na Argentina din mai shekara 29. (Fabrizio Romano, Twitter)
Nottingham Forest na gab da kammala yarjejeniyar daukar dan wasan tsakiya kuma na baya na Faransa, Moussa Niakhate, mai shekara 26, tuni sun kusan kammala batun kudin da za a kashe na musayar shi da Mainz. (Fabrizio Romano, Twitter)
Da alama lokaci ya kurewa Crystal Palace, kan son daukar dan wasan Wolves, kuma na tsakiyar Ingila Morgan Gibbs-White, mai shekara 22, kan £20m. (Sunday Sun)