Man City na gab da saye Echeverri, Arsenal na zawarcin Inacio

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na gab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan Argentina da ke taka leda a River Plate, Claudio Echeverri mai shekara 17 a wani tsari da zai ba su damar daukan aron ɗan wasan har zuwa karshen kakar Firimiyar bana. (ESPN)
Arsenal na son cimma yarjejeniya da ɗan wasan Sporting Lisbon mai shekara 22, Goncalo Inacio a watan Janairu, yayinda ɗan wasan na Portugal da ke iya tafiya wata kungiya kan yuro miliyan 60 bisa yarjejeniyar da yake kai a yanzu, ya ja hankalin Liverpool. (A Bola - in Portuguese)
Ana alakanta ɗan wasan Sporting Lisbon Viktor Gyokeres mai shekara 25 da Arsenal da Chelsea a watan Janairu, sai dai ɗan wasan na Sweden ya nuna ya fi son cigaba da zama a ƙungiyar na Portugal har zuwa karshen kaka. (Record, via 90 Min)
Tottenham ta shirya biyan fam miliyan 25 kan ɗan wasan Belgium mai shekara 18 da ke buga tsakiya, Arthur Vermeeren daga Royal Antwerp. (Sun)
Tsohon ɗan wasan tsakiya a Ingila da Manchester United Jesse Lingard, mai shekara 31, ya samu tayi daga ƙungiyar Lille da ke buga Ligue 1. (Mirror)
Manchester United na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Netherlands mai shekara 22, Joshua Zirkzee kan fam miliyan 26. Ɗan wasan ya zura kwallaye bakwai a wasanni 17 a Serie A. (Sport1 via Metro)
Inter Milan na son saye ɗan wasan Iran Mehdi Taremi, mai shekara 31 daga Porto a watan Janairu, sannan za su nazarci ɗan wasan Manchester United Anthony Martial, mai shekara 28, da Armando Broja, mai shekara 22 daga Chelsea. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Atletico Madrid ta bi sahun Juventus a farautar ɗan wasan Argentina Rodrigo de Paul, mai shekara 29. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Paris Saint-Germain ta amince da yarjejeniyar yuro miliyan 20 kan ɗan wasan Brazil mai shekara 18 Gabriel Moscardo. (Fabrizio Romano)
Tsohon ɗan wasan Faransa Raphael Varane, mai shekara 30, ya shirya barin Manchester United zuwa Lens, inda ya soma haskawa. (L'Equipe - in French)
Ɗan wasan Brazil da ya taba taka leda a Athletico Paranaense, Vitor Roque mai shekara 18, ya tafi Sifaniya domin soma haskawa a Barcelona. (Fabrizio Romano)













