Real ta koma ta 18 bayan doke Atalanta a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta je ta doke Atalanta da cin 3-2 a wasa na shida a Champions League da suka fafata ranar Talata a Italita.
Ƙungiyar Sifaniya ta ci ƙwallayen ta hannun Kylian Mbappe da Vinicius Junior da kuma Jude Bellingham.
Ita kuwa Atalanta mai masaukin baƙi ta zare biyu ta hannun De Ketelaere da kuma Ademola Lookman.
Wannan shi ne karo na huɗu da suka fafata a tsakaninsu a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai a tarihi.
Kafin fara kakar bana, Real Madrid ta doke Atalanta 2-0 ta lashe Uefa Super Cup cikin Agustan 2024.
Sun kuma kara a kakar 2020/21 a Champions League, inda Real Madrid ta je Italiya ta ci 1-0 ranar Laraba 24 ga watan Fabrairun 2021.
A wasa na biyu kuwa Atalanta ta kwaso ƙwallo 3-1 a Sifaniya ranar 14 ga watan Agustan 2021.
Da wannan sakamakon Real Madrid ta yi sama zuwa mataki na 18 a Champions League da maki tara, bayan cin wasa na uku da rashin nasara uku.
Atalanta kuwa mai maki 11 ta yi kasa zuwa ta tara a teburi, bayan nasara uku da canjaras biyu an doke ta wasa ɗaya.
Ranar Talata 21 ga watan Janairu, Atalanta za ta karɓi bakuncin Sturm Graz, ita kuwa Real Madrid za ta fafata da Red Bull Salzburg ranar Laraba 22 ga watan Janairun 2025.
Wasa da aka yi tsakanin Atalanta da Real Madrid:
Champions League Talata 10 ga watan Disambar 2024
- Atalanta 2 - 3 Real Madrid
European Super Cup Laraba 14 ga watan Agustan 2024
- Real Madrid 2 - 0 Atalanta
Champions League Talata 16 ga watan Maris 2021
- Real Madrid 3 - 1 Atalanta
Champions League Laraba 24 ga watan Fabrairu 2021
- Atalanta 0 - 1 Real Madrid
Ƴan wasan Real Madrid da ta je da su Atalanta:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin, Sergio Mestre.
Masu tsare baya: Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Rüdiger, Asencio, Youssef, D. Jiménez.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos, Chema.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim.











