Yadda aka yi musayar fursunoni mafi girma a duniya tun bayan yaƙin cacar-baka

    • Marubuci, Steve Rosenberg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Russia editor
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

“Wannan batu ne da ya fi dacewa a yi shi cikin sirri.”

Wannan ita ce kalmar da jami'an Rasha suka furta lokacin da aka nemi su yi magana a kan yuwuwar musayar fursunonin tsakanin yammaci da gabashin duniya.

Wadannan su ne kalaman da muka yi ta ji tsawon watanni.

Yadda fadar gwamnatin Rasha ke son a yi yarjejeniyar kenan, a yi ta cikin sirri ba a gaban 'yanjarida ba.

Tattaunawa tsakanin jami'an sirri da kuma gwamnati da gwamnati.

Haka aka yi ta yi har sai Rasha ta samu abin da take so ko kuma wa take so ta samu a sakar mata.

Amma duk da cewa cikin sirri aka rika wannan tattaunawa da yarjejeniya, akwai alamu da suka rika nuna cewa lallai akwai wani abu da ke gudana.

A wata hira da tsohon danjaridar gidan talabijin na Fox News, Tucker Carlson, a watan Fabarairu da ya wuce Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi magana a kan Evan Gershkovich, wakilin mujallar Wall Street Journal, wanda aka tsare a Rasha da tuhumar laifin leken asiri.

“Ba na kawar da ywuwar cewa Mista Gershkovich ka iya komaw kasarsa,” in ji Mista Putin.

Shugaban ya kara da cewa: “Muna son jami'an Amurka na musamman su duba su ga yadda za su iya bayar da gudummawa wajen cimma bukatun jami'anmu na musamman.”

Wannan wata alama ce da ta nuna wa jama'a cewa lallai wani abu na gudana: Gwamnatin Rasha a shirye take a yi yarjejeniya da ita

Shugaban na Rasha bai ambaci sunaye ba. Amma dai ya nuna karara wanda yake son a sako wa kasarsa idan za a yi wannan musaya: Mutumin kuwa shi ne, Vadim Krasikov, wanda ake zargi jami'in leken asiri ne, wanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari na rai da rai bisa laifin kisan kai - ba a Amurka ba, a Jamus.

Bayan 'yan kwanki da wannan magana, sai jagoran 'yan hamayya na Rasha Alexei Navalny ya rasu a wani gidan yari.

Kafin rasuwarsa, ana shirin fara tattaunawa kan musayarsa, da Evan Gershkovich da kuma tsohon sojan Amurka na musamman Paul Whelan, dukkanninsu suna tsare ne a gidajen kurkuku na Rasha, inda za a yi musayarsu da Vadim Krasikov da ke tsare a Jamus.

Dama Jamus ta shiga wata tattaunawa ne ta yarjejeniyar musayar fursunoni?

Idan muka yi gaba zuwa watan Yuni. Shari'ar sirri ta Evan Gershkovich kan laifin leken asiri - wadda mujallar Wall Street Journal da gwamnatin Amurka suka shashantar da cewa ba ta gaskiya ba ce - sai kawai aka ga an fara ta a Yekaterinburg. Nan da nan aka dage shari'ar har zuwa tsakiyar watan Agusta.

Amma a watan da ya gabata, ba zato ba tsammani sai kotun ta matso da zama na biyu na shari'arsa da sama da mako uku. A shari'ar da aka yi cikin sauri - kwana uku, an yanke wa, Evan Gershkovich hukuncin zaman gidan yari na shekara 16 a wani gidan kaso na ƙare-kukanka.

Haka kuma a wannan rana wata kotu a Kazan ta yanke wa 'yarjaridar Amurka mai asali a Rasha, Alsu Kurmasheva, hukuncin daurin shekara shida da rabi. An yi shari'ar tata ne cikin kwana biyu kawai.

Duka wannan ya nuna cewa akwai wanda yake cikin wani sauri. Kuma wannan ita ce babbar alama da ta nuna cewa an cimma wata yarjejeniya, kila za a yi musayar fursunoni. Yawanci jami'an Rasha suna sanya sharadin yanke wa mutum hukunci a yarjejeniyar musayar fursunoni - wato sai kotu ta yanke masa laifi kafin a yi musayar.

A farkon makon nan aka kara ganin alamu tare da rahotannin da ke nuna cewa an sauya wa wasu jerin fitattun fursunonin siyasa na Rasha wajen da ake tsare da su a gidan kaso na kare-kukanka da wasu wurare.

Haka aka rika samun karuwar jita-jita. To ko wannan zai iya kasancewa wani bangare na wata babbar musayar fursunoni sama da wadda aka yi tsammani tun da farko?

Kwatsam aka ji labari a Belarus, cewa Shugaban Ƙasar Alexander Lukashenko ya yarda ya yafe wa Rico Krieger, wani dan kasar Jamus da aka yanke wa hukuncin kisa kan laifin ta'addanci da wasu tume-tuhume. Ko yana cikin wadanda aka yi musayar da su?

Yanzu dai mun sani cewa, wannan ce musayar fursunoni mafi girma tun bayan yakin cacar-baka tsakanin ƙasashen Yamma da na gabashin duniya.

Gwamnatocin kasashen yammacin duniya za su yi maraba da sakin 'yan kasarsu da kuma samun 'yancin wasu daga cikin fitattun fursunonin siyasa na Rasha.

Haka ita ma gwamnatin Rasha za ta yi maraba da komawar jami'anta na leken asiri.

Dukkanin bangarorin biyu za su iya ikirarin cewa yarjejeniya ce mai kyau da alfanu.

Amma idan har Rasha ta zartar da cewa kamar yadda ta taba yi a baya, cewa diflomasiyyar (musayar) fursunoni, na aiki, to abin damuwar shi ne da wuya a ce wannan shi ne lokaci na karsh da za a yi ko aka yi amfani da fursunoni na waje da kuma Rashawa a matsayin wata hanya ta cimma wani buri ko manufa.

Kenan wannan za ta ko kuma ta zama wata kafa ta cimma muradu.