Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Al'ummar Musulmi na bikin Sallar Azumi
A ranar Juma'ar nan ne al'ummar Musulmi a wasu kasashen duniya ke bikin Sallar Azumi bayan kammala azumin watan Ramadana da ya kasance mai kwana 29.
Hukumomin Saudiyya sanar da ganin watan Shawwal da yammacin Alhamis wanda hakan ya kasance karshen watan Ramadan ke nan.
Sannan Najeriya da Nijar da kuma wasu kasashe su ma suka bi sahun Saudiyyar wajen sanar da ganin watan na Shawwal a ranar Alhamis.
To sai dai yayin da wadannan kasashe da ma wasu suke yin Sallar Idin Azumin a ranar Juma'ar nan, hukumomin Iran su kuwa sun ce sai ranar Asabar za a yi Sallar a kasar saboda ba su ga watan na Shawwal ba.
A Najeriya tun da farko Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ne ya sanar da ganin jinjirin watan na Shawwal a wasu sassan kasar.
Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce ganin jinjirin watan da aka yi a a kasar ya sanya ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1444.
Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Maigirma Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan a bana.
Cikin sanarwar da ya yi Sarkin Musulmi ya ce "mun samu bayanai daga wurare daban-daban a Najeriya kuma mun zauna da masana domin tabbatar da ingancin waɗannan bayanan gabanin mu sanar da al'umma cewa an ga watan.
Gwamnatin Najeriyar ta bayar da hutun kwana biyu ranar Juma'a 21 ga watan Afirilu da kuma Litinin 24 ga watan na Afirilu 2023.
Can ma a Jamhuriyar Nijar hukumomi sun tabbatar da ganin jaririn watan Shawwal a ranar Alhamis.
An ga watan sallar ne a jihohin Diffa da Dosso da Zinder da Agadez da Tahoua da ku ma Tillabery.
Majalisa ƙoli kan harkokin addinin Musulunci ta ƙasar ta Nijar ce ta bayar da sanarwar ganin watan.