Arsenal ta ci gaba da zama ta biyu bayan cin Chelsea a Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta yi nasara a kan Chelsea da cin 1-0 a gasar Premier League karawar mako na 29 da za su kece raini a Emirates ranar Lahadi.

Mikel Merino ne ya ci wa Gunners ƙwallon a minti na 20, hakan ya bai wa ƙungiyar maki ukun da take bukata.

Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier da maki 58, ita kuwa Chelsea mai maki 49 tana ta huɗu a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

Wannan shi ne wasa na biyu da suka fuskanci juna a kakar nan, bayan tashi 1-1 ranar Lahadi 10 ga watan Nuwambar 2024 a Stamford Bridge a Premier League.

Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a karawa bakwai baya a Premier League da Chelsea, inda Gunners ta ci wasa biyar da canajaras biyu.

Chelsea ta yi rashin nasara karo na uku a jere a hannun Gunners a Emirates a Premier League.

Arsenal ta ci wasa na biyu daga fafatawa shida a dukkan karawa da yin canjaras uku daga ciki.

Wasa uku Chelsea ta yi nasara daga 20 a waje da ta yi da ƙungiyoyin da ke samanta a kan teburi da canjaras uku aka doke ta 14.

ranar Talata 1 ga watan Afirilu, Arsenal za ta kara da Fulham a wasan hamayya a Emirates daga nan ta je Everton ranar Asabar 5 ga watan Afirilu.

Ita kuwa Chelsea za ta yi wasa mai zafi da Tottenham a Stamford Bridge ranar 3 ga watan Afirilu, sannan ta je Brentford ranar Lahadi 6 ga watan Afirilu.