Hamas ta tabbatar da mutuwar shugaban sojinta

Asalin hoton, AFP
Hamas ta tabbatar da kashe shugaban sojinta, Mohammed Deif.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Alhamis ta kuma bayyana mutuwar mataimakin kwamandan sojin ƙungiyar Marwan Issa.
A watan Yulin shekarar da ta gabata ne sojojin Isra'ila suka ce sun kashe shi Deif, amma sai a yanzu ne ƙungiyar Hamas ɗin ta tabbatar da kisan nasa.
Isra'ila ta ce Deif na ɗaya daga cikin waɗanda suka kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a kudancin Isra'ila, inda aka kashe Isra'ilawa 1,200 tare da yin garkuwa da 251.
Ana kallon Deif a matsayin mutum na biyu mafi girman matsayi a ƙungiyar Hamas a Gaza, bayan Yahya Sinwar, shugaban ƙungiyar a yankin Gaza, wanda shi ma sojojin Isra'ila suka kashe shi a shekarar da ta gabata.
A shekarar da ta gabata ne alƙalan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, suka fitar da sammacin kama Deif, tare da firaministan ISra'ila Benjamin Netenyahu da kuma tsohon ministan n tsaron Isra'ila, Yoav Gallant.
Deif ya yi fice wajen taimakawa wurin gina hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da mayaƙan Hamas ke amfani da su wajen shiga Isra'ila.

Asalin hoton, Media sources
Harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ne aka fara yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas.
Hare-haren da sojojin Isra'ila suka kwashe wata 15 suna yi a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar Falasɗinawa fiye da 47,460, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Gaza ta bayyana.
A ranar 19 ga watan Janairu ne yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin ta fara aiki.
Kawo yanzu an saki Isra'ilawa 15 da Hamas ta yi garkuwa da su.
Ya zuwa yanzu an sako fursunonin Falasɗinawa 400, kama daga waɗanda ke zaman shekaru masu yawa saboda laifukan tayar da bama-bamai da sauran hare-hare zuwa matasan da ake tsare da su ba tare da wata tuhuma ba.
Da dama sun koma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da gabashin Birnin Kudus da kuma Gaza, yayin da aka fitar da kusan 70 masu manyan laifuka zuwa wasu ƙasashen.










