Rawa da kallon gasar Kofin Duniya na cikin hotunan Afirka na mako

An wallafa

Zaɓaɓɓun hotunan Afirka na mako da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Lahadi a Afirka ta kudu, wasu mata daga cocin Nazareth Baptist ke rawar nuna haɗin kai
,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubban mutane ne suka taru domin yin addu'o'i da bikin sasanto a fadar sarkin Zulu ta Enyokeni da ke Nongoma ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai wannan rana a gasar cin Kofin Duniya da ke gudana a Qatar, wani magoyin bayan tawagar ƙasar Morocco ke tsokanar magoya bayan ƙasar Belgium bayan da ƙasar ta yi nasar da ci 2-0
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, washe gari ne kuma Senegal ta casa ƙasar Ecuador da ci 2-1 inda ta samu gurbi a wasan zagayen gaba
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Senegal ce ƙasa ta biyu a Afirka bayan Morocco, da ta samu tsallakawa zuwa zagayen gaba a gasar
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mostafa Mahmoud, mai shekara 68, tsohon ɗan kwallon Masar ne. Kuma ya kwashe kusan shekara 50 yana gudanar da kamfanin ƙera bal.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne kuma waɗannan matan ke rawa a yayin buɗe gangamin yaƙi da cin zarafin mata wanda za a kwashe kwana 16 ana gudanarwa a ƙasar Laberiya
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai sayar da kayan miya a wata kasuwa a ƙasar Tunisiya kenan ranar Alhamis yayin da yake tsaka da kasuwancinsa
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin kuma wannan matar 'yar ƙasar Masar ke sana'ar saƙa wajen rataya tufafi.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Lupita Nyong 'yan wasan fina-finai a Kenya ta halarci wani wani biki da aka gudanar a birnin New York na Amurka ranar Asabar
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a Kongo - waɗanda ke kiraye-kirayen sojojin ƙasar su kawo ƙarshen 'yan tawayen da ke addabar arewacin lardin Kivu - sun yi arangama da jami'an 'yan sanda ranar Alhamis
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Laraba kena wani yaro ke noma gonarsa a ƙasar Kenya.