Alkalan wasan Man United da Wolves ba za su busa Premier League ba

Asalin hoton, Getty Images
Simon Hooper da Michael Salisbury da kuma Richard West ba za su busa gasar Premier League ba a karshen makon nan.
Hakan ya biyo bayan zargin fenatiri da Wolverhampton ta samu, amma ba su bayar da a karawar da United ta ci 1-0 ranar Litinin.
Wolves ta ce ya kamata a ba ta bugun daga kai sai mai tsaron raga a karin lokaci, bayan da golan United, Andre Onana ya doki kan Sasa Kalajdzic a lokacin da zai fitar da kwallo.
Wasan an tashi United ta ci 1-0, yayin da Hooper shine rafli, Salisbury da West, suna suka kula da na'ura mai taimakawa alkalin tamaula yanke hukunci VAR.
Kociyan Wolves, Garry O'Neil ya ce rashin bayar da fenariti da rafli bai yi ba ya nuna alamar tambaya ga yadda ake amfani da VAR, ya kara da cewar alkali Jon Moss mai kula da alkalan Premier League ya nemi gafara bisa kuskuren da aka yi.
''Jon Moss ya fara fenariti ne karara da ya kamata a bayar '' kamar yadda O'Neil ya sanar da manema labarai.
...Sai dai ya kamata da Jon ya fito ya sanar cewar fenariti ne da cewar an ci karo da cikas ne - ya yi mamaki da alkalin cikin fili da bai hura ba, sannan VAR ba ta fayyace gaskiya ba.
An dakatar da Salisbury wasanni da yawa a Afirilu, bayan da aka hana Brighton fenariti a karawar da Tottenham ta ci 2-1 a gasar Premier League.












