Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Monaco ta kammala ɗaukar Balogun daga Arsenal
Monaco ta kammala sayen dan wasan gaba Folarin Balogun kan fan miliyan 35 daga Arsenal kan kwantiragin shekara biyar.
Dan wasan na Amurka mai shekara 22 ya koma Faransa bayan ya ci kwallaye 22 a matsayin aro a Reims a kakar wasan da ta wuce.
Balogun bai buga wa Arsenal wasa a gasar Premier ba a farkon kakar bana duk da cewa dan wasan gaba Gabriel Jesus ya ji rauni.
Ya rattaba hannu a kan kwantiragi da Arsenal yana da shekara 17 kuma ya buga wasanni biyu a lokacin da yake tare da kungiyar.
A rashin Jesus, Eddie Nketiah ne ya fara wasa biyu na farko na wannan kakar, yayin da Leandro Trossard ya samu shiga wasan da suka tashi 2-2 da Fulham ranar Asabar.
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na intanet, Arsenal ta ce: "Muna godiya ga Folarin bisa gudunmawar da ya bayar ga Arsenal, daga bangaren matasa har zuwa babbar kungiyar, muna kuma yi masa fatan alheri da farin ciki a sabon babinsa a Monaco."
Haifaffen New York, Balogun ya koma Landan tun yana karami kuma ya fara wasa ne a bangaren matasan Arsenal.
Ya buga wa kungiyoyin Ingila wasa har zuwa ’yan kasa da shekara 21, inda ya buga13 a wannan matakin, kafin ya zabi buga wa Amurka wasa a matakin manya.
Balogun ya yi zaman aro a Middlesbrough da Reims, kuma an alakanta shi da Chelsea kafin Arsenal ta amince da tayin Monaco.