Abu huɗu daga sabbin takardu kan kisan tsohon shugaban Amurka, John F Kennedy

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Sabbin takardun bayanai fiye da 2,000 da aka fitar da ke da alaƙa da bincike kan kisan gilla da aka yi wa Shugaba John F Kennedy sun yi fice ne ba wai kawai saboda bayanan da ke ƙunshe a cikinsu ba, har saboda bayanan da aka cire.

Kamar yadda ƙwararru suka yi hasashe, sabbin takardun bayanan da gwamnatin Trump ta saki ba su amsa dukkanin tambayoyin da ake da su ba kan wani babban lokaci mai cike da tarihi a Amurka wato kisan Kennedy a Dallas a shekarar 1963.

Sai dai a wannan karon, an haɗa da takardun da ba a ɓoye komai ba ko kuma ba a boye abubuwa sosai ba - an sanya takardun ainihi maimakon waɗanda aka kulle wasu wurare ko kuma aka bar wasu wuraren babu komai.

Wani binciken gwamnatin Amurka ya nuna cewa Lee Harvey Oswald, wani mai yawace-yawace kuma tsohon sojan ruwa a Amurka wanda a wani lokaci ya kuma tarayyar Soviet, shi kaɗai ya yi aikin a lokacin da ya harbi jerin motocin Kennedy daga wani gini da ke kusa.

Sai dai har yanzu wannan batu na ɗiga ayar tambaya tare da shaci faɗi masu ban mamaki, fiye da shekara 60 bayan kisan - kuma sabbin bayanan da aka fitar ba lallai su sauya hakan ba.

Ga wasu daga cikin muhimman abin da muka kalato.

Ƙarin bayani kan Oswald

Masana da dama sun jinjina sakin bayanan a matsayin wani mataki na samun bayanan gaskiya.

A baya, an fitar da dubun dubatar takardun bayanai amma wasu ɓangarori an tace su an ɓoye. Wasu kuwa ba a ma fitar da su ba, inda a cewar hukumomi saboda tsaron ƙasa ne.

Wasu daga cikin sabbin bayanan a baya an fitar da su, amma a yanzu an fitar da waɗanda suka fi su kammala. Duk da dai ƙwararru na ci gaba da yi musu tsifa da taza, zuwa yanzu ba a gano wani labari mai girgiza ƙasa ba.

Duk da haka, Jefferson Morley, wani tsohon ɗan jarida a Washington Post kuma Editan JFK Facts, ya ce wannan shi ne '' labari mafi daɗi kan bayanan JFK tun shekarun 1990''.

'' Takardun bayanai da dama masu muhimmanci sun fito fili ga jama'a,'' in ji shi.

Takardun sun kuma ƙara haske kan sa idon da hukumar leƙen asiri ta Amurka (CIA) ta yi kan Oswald, in ji Morley, wanda ya ce a ƴan shekarun baya ne aka san girmar bibiyarsa da suka yi.

'' Ya kasance abin bincike mai muhimmanci ga CIA'' tun kafin ma ya yi kisan, a cewar sa.

Philip Shenon, wanda ya rubuta wani littafi a 2013 kan kisan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa takardun da aka fitar a baya sun bayyana wata tafiya da Oswald ya yi zuwa birnin Mexico a 1963, watanni kafin lokacin kisan.

CIA na bibiyarsa a lokacin, in ji shi, a cewar AP. " Akwai dalilan da za su sa a yarda cewa ya yi maganar kashe Kennedy a fili a birnin Mexico kuma wasu mutane sun jiyo shi ya na faɗi.''

A wani bayani da suka fitar a watan Afrilun 1975, hukumar leƙen asiri ta CIA ta nuna ba ta san abubuwa sosai ba kan tafiyar da Oswald ya yi zuwa Mexico, in ji AP.

Hukumar ta CIA ta naɗi magana ta waya da Oswald ya yi tsakaninsa da wani mai yin gadi a ofishin jakadancin Soviet har sau uku, sai dai a waya ɗaya ne kawai Oswald ya faɗi sunanshi.

Bayani kan hanyoyin tattara bayanan sirri

Wasu daga cikin takardun sun bayyana alaƙar Kennedy da hukumar leƙen asiri ta Amurka CIA kafin mutuwarsa da kuma hanyoyin tattara bayanan sirri - wanda ya bayar da damar ayyukan yaƙin cacar baka.

Wani sabon bayani da suka fitar da ba a ɓoye komai ba ya nuna cikakken samfurin wata takarda da mai taimakawa Kennedy, Arthur Schlesinger ya rubuta.

Takardar ta nuna yadda hukumar ta kankane ofisoshin jakadancin Amurka har a ƙasashen ƙawayenta kamar Faransa.

A cikin takardar, Schlesinger yana gargaɗin Kennedy kan tasirin da hukumar ke da shi kan tsare-tsaren Amurka na ƙasashen waje. Duk da dai ba su da alaƙa kai-tsaye da kisan, takardar ta bayyana alaƙa mara daɗi tsakanin shugaban da hukumomin leƙen asiri.

A bisa tsari, hukumar CIA ba ta yarda da fitar da bayanai kan ayyukanta ko kuɗaɗen da take kashewa ba, in ji David Barrett, wani farfesa a jam'iar Villanova kuma ƙwararre kan CIA da ƙarfin ikon shugaban ƙasa.

''Abu ne mai kyau gwamnati ta saki waɗannan bayanan ko da za a kulle wani ɓangare,'' in ji shi.

Ɗaya daga cikin bayanan na nuna yadda ake amfani da Fluoroscopic scanning- ta hanyar amfani da na'urar X-ray domin nuna hotunan cikin wani abu.

An ƙirƙiro wannan tsarin ne domin taimakawa wajen gano ɓoyayyun na'urorin magana waɗanda ake ganin ana dasawa a ofisoshin hukumar CIA.

A wata takardar, hukumar CIA ta bayyana wani shiri da ake sanya alama domin gane akwatin waya na bainar jama'a da ake tatsar bayanai, ta hanyar amfani da wani fenti da ba a iya gani sai a ƙarƙashin wani haske.

Takardar ta kuma yi fice saboda wani suna da ke cikinta - James McCord, wanda daga baya aka sanshi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka shiga ginin Watergate ba bisa ƙa'ida ba.

Shigarsu ginin ne ya taso da bankaɗo rikicin da ya yi sanadiyar kifar da shugaba Richard Nixon.

Tsofaffin ra'ayoyin sun yi kome

Wasu daga cikin sanannun shafukan da ke intanet suna iƙirarin cewa sabbin takardun sun fito da sabbin bayanai akan ƙulla kashe Kennedy da aka daɗe ana zargin yi - duk da dai wasu daga cikin waɗannan bayanan sun shafe shekaru da fitowa fili.

Sun haɗa da bayanai da aka wallafa da suka yaɗu kan Gary Underhill - wani jami'in leƙen asiri na sojoji a yaƙin duniya na biyu.

A cewar rahotanni, Mista Underhill ya yi ikirarin cewa wata ƙungiyar jam'ian CIA ne ke da alhakin kisan, wani ra'ayi da aka wallafa a jaridar Ramparts a 1967.

An bayyana mutuwar Mista Underhill a 1964 a matsayin kisan kai, sai dai jaridar ta nuna shakku kan hakan ma.

Hotunan wata takarda mai shafi shida kan Mista Underhill ya yaɗu sosai a ranar Talata- sai da ɓangare da dama daga ciki ba sabbin bayanai bane. An daɗe ana tattaunawa kan labarinsa a intanet da kuma takardar da ke magana kan labarinsa an fara fitar da ita ne a 2017.

Wasu jimloli a ɗaya daga cikin shafukan takardar ne kawai a yanzu aka bayyana cikin sabbin takardun da aka saki.

Kuma dai an samu labarin ne daga majiyoyi ba daga waɗanda suka ga abin ba bayan mutuwar Underhill, kuma babu wata shaida ƙwaƙwara.

Sai dai labarin na ɗaya daga cikin labarai marasa tushe da ke yawo bayan sakin takardun.

Ko ba a rage komai a takardun ba?

Wata doka ta shekarar 1992 ta buƙaci a saki dukkan takardun da ke da alaƙa da kisan cikin shekara 25 - sai dai dokar ta kuma ce banda waɗanda za su shafi tsaron ƙasa.

Ƙarin buƙatar da ake da shi na a bayyana gaskiya ya kai ga sakin wasu bayanan cikin shekaru - Shugaba Trump a wa'adinsa na farko da kuma shugaba Biden a shekarar 2023, sun saki takardun rukuni rukuni.

Gabanin sake waɗannan sabbin takardu, shugaba Trump ya umurci ma'aikatansa da kada su ɓoye komai daga cikin takardun.

Sia dai ba hakan aka yi ba, har yanzu akwai wasu ɓangare da aka ɓoye a sabbin takardun. Sai dai ƙwararru da dama sun amince cewa sabbin takardun da aka samu wani matakin gaba ne na bayyana gaskiya.

Ɗan jarida na JFK Files, Morley, ya ce akwai sauran takardun da ke wurin ajiya na ƙasa da har yanzu ba a saki ba, akwai wasu kuma da hukumomin CIA da FBI ke riƙe da su da har yanzu ba su bayar ba.

Duk da dai akwai yiwuwar za a saki wasu takardun nan gaba - da kuma alƙawarin sakin bayanai kai kisan Robert F Kennedy Sr da Martin Luther King Jr - tambayoyin da ake yi kan kisan JFK tabbas za su ci gaba.

"Duk sanda aka yi kisa za ayi ta samun muhawara har a wasu lokutan ma a samu shaci faɗi, '' In ji Barrett, masanin tarihin Villanova. ''Kuma hakan ba zai canza ba saboda waɗannan takardun ko wasu daban.''