Gasar wasan keken guragu ta mata da mai ninƙaya cikin hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin ƙayatattun hotunan sassa daban-daban na Afirka na mako:

Matashiyar dauke da murmushi a fuskarta.

Asalin hoton, MICHAEL TRAN/AFP

Bayanan hoto, Tauraruwar fina-finai ta Afirka ta Kudu, Thuso Mbedu, lokacin da ta halarci dabdalar da aka shirya bayan kammala aikin 'Charlize Theron Africa Outreach' da masana'antar Hollywood ta Amurka ta shirya a ranar Asabar.
Mace ta wuce zanen fuskar Nelson Mandela.

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Wata mace ɗauke da kaya a kanta, ta wuce bangon da a ka yi zanen Nelson Mandela a birnin Cape Town, Afirka ta Kudu, a wani ɓangare na bikin cikarsa shekara 106 in da yana raye.
Wani mutum na kayata tebur da leda launin tutar Rwanda

Asalin hoton, LUIS TATO/AFP

Bayanan hoto, Wani mutum na ƙawata tebur da leda mai launin tutar ƙasar Rwanda, a wata mazaɓa da ke birnin Kigali, gabannin zaɓen shugaban kasa. An ayyana shugaba Paul Kagame a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kashi 99 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a ranar Laraba. Zaɓen da masu rajin kare hakkin ɗan adam da 'yan adawa suka yi kakkausar suka akai.
 Yui Kamiji 'yar Japan da Kgothatso Montjane ta Afirka ta Kudu

Asalin hoton, DANIEL KOPATSCH/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, gwarazan wasan Tennis Kgothatso Montjane daga Afirka ta Kudu, da Yui Kamiji 'yar Japan suka lashe kyauta a wasan ƙarshe na keken guragu ma a Wimbledon a Birtaniya.
Matasa na wasan ninkaya a teku.

Asalin hoton, HAZEM GOUDA/AFP

Bayanan hoto, Masuwasan ninƙaya kenan a tekun birnin Al-Askandariyya da ke ƙasar Masar a ranar Juma'a.
Butum-butumin sarki Tutankhamun.

Asalin hoton, ZHANG HENGWEI/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Butum-butumin sarki Tutankhamun, na ɗaya daga cikin kayan tarihin ƙasar Masar da aka nuna a baje kolin gidan adana kayan tarihi na birnin Beijing a kasar China, a ranar Laraba.
Mata biyu zaune dauke da murmushi a fuskarsu.

Asalin hoton, OUPA BOPAPE/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Taurarin wasan kwaikwayon tarihi na Afirka ta Kudu, mai suna Sarauniya Modjadji - Makoma Komie Mohale (hagu) da Masutang Resekele (dama), sun fito a matsayin uwa da 'ya a cikin wasan, inda suka kalli haska shirin a karon farko a birnin Johannesburg ranar Juma'a.
'Yan sandan Kenya sun hau layin shiga jirgi.

Asalin hoton, GUERINAULT LOUIS/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ƙarin 'yan sandan Kenya 200, sun isa Haiti, inda aka tura su domin magance matsalar tsaron da ake fama da ita a can. Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da 'yan daba suka karbe iko da yawancin ƙasar da kashe-kashen mutane da kona gidaje da cin zarafin farar hula.
Dan bamben Ghana Abdul Razak Alhassssan da Cody Brundage na Amirka

Asalin hoton, JOSH HEDGES/AFP

Bayanan hoto, Ɗan wasan damben UFC ɗan ƙasar Ghana, Abdul Razak Alhassan (hagu) yana fuskantar abokin karawarsa Cody Brundage a Amurka a ranar Asabar.
Mawaki dan Kamaru da Faransa Yame akan dandamali.

Asalin hoton, SEBASTIEN SALOM-GOMIS/AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a mawaƙi ɗan Kamaru da Faransa Yamê ya na cashewa a bikin kalankuwar mawaƙa a Vieilles Charrues a yammacin Faransa.
Matashiya dauke da wutar gasar Olympic.

Asalin hoton, GEOFFROY VAN DER HASSELT/AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin a birnin Paris, wata matashiyar 'yar wasan kwaikwayo 'yar Faransa da Ivoria Coast mai suna Claudia Tagbo ɗauke da wutar gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta Olympic
Matashi akan keke a gabar teku.

Asalin hoton, FEISAL OMAR/REUTERS

Bayanan hoto, Wannan matashin na cike da nishaɗi a kan kekensa, a bakin tekun Lido da ke babban birnin kasar Somalia Mogadishu, a ranar Asabar.
Mota na tafiya akan titin da bishiyoyi sukai wa rumfa.

Asalin hoton, HAKAN NURAL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Talata, wata mota ce nan ke tafiya a kan titin da bishiyoyi suka yi wa rumfa a birnin Harare na Zimbabwe.