Haaland ya ta da hankalin Man City, Barcelona za ta aro Messi

Erling Haaland

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Erling Haaland yana da burin tafiya Real Madrid
An wallafa

Manchester City na sane cewa ɗan gabanta Erling Haaland yana da burin taka leda a Real Madrid amma kuma take son tattaunawa da shi kan tsawaita kwantiraginsa da zai ƙare a watan Yuni na 2027. (ESPN)

Barcelona na duba yiwuwar ɗauko aron Lionel Messi, a watan Janairu idan ƙungiyarsa Inter Miami ta kasa samun gurbin wasannin Kofin Amurka na MLS. (Sport daga Mail)

Chelsea na jira ta ga ko ɗan gaban Najeriya, Victor Osimhen zai ƙulla sabuwar yarjejeniya da Napoli, kasancewar har yanzu shi da wakilinsa ba su yanke shawara ba kan ci gaba da zamansa a ƙungiyar ta Italiya. (90 Min)

Brentford na duba yuwuwar zawarcin ɗan wasan tsakiya na Southampton Carlos Alcaraz a watan Janairu, kasancewar daman tun a watan Janairu ƙungiyar ta rasa ɗan Argentinan - za ta neme shi ne duk da cewa matashin mai shekara 20 ya ƙulla sabuwar yarjejeniya a ranar Juma'a. (Standard)

Ƙungiyar Burton Albion ta sanya wani saƙo a intanet inda take barkwanci a game da rahotannin da ke cewa tsohon ɗan wasan Liverpool, da Tottenham, da tawagar Ingila Peter Crouch mai shekara 38 zai koma taka leda. (Mail)

Tsohon ɗan wasan Jamus Jerome Boateng, mai shekara 35, ya rasa ƙungiyar da za ta ɗauke shi bayan da ya kasa samun kwantiragi da tsohuwar ƙungiyarsa Bayern Munich. (Sun)

Ana jarraba tsohon ɗan wasan gaba na gefe na Tottenham, da Crystal Palace da kuma Ingila Andros Townsend, a ƙungiyar Luton Town, kuma sabuwar zuwan Premier na dab da ɗaukansa. (Express)

Ana matuƙar mamakin yadda sunan tsohon kocin Swansea, da Leeds United Garry Monk ya kasance a matsayin wanda ake cewa zai iya maye gurbin Andrea Pirlo a Sampdoria. (SampNews24, daga Sun)

Brighton na shirin fara tattaunawa da ɗan gaban Ingila Danny Welbeck, mai shekara 32, a kan sabon kwantiragi. (Football Insider)

Ɗan bayan Crystal Palace Tyrick Mitchell, na tunanin daina taka wa Ingila wasa, domin komawa tawagar Jamaica. (Mail)

Bradford City na harin Steve Thompson da Neil Redfearn a neman sabon kocin da ƙungiyar ke yi domin maye gurbin Mark Hughes. (Star)