Real da Chelsea da United da Liverpool na rige-rigen daukar Bellingham

An wallafa

Arsenal na kila-wa-kala kan dan kwallon Portugal, Xeka, wanda bai da kungiya a yanzu, bayan da aka yi mata tayin tsohon dan wasan Lille mai buga tsakiya mai shekara 27, wanda aka gabatarwa da wasu kungiyoyin Premier League. (90min)

Real Madrid na shirya shan gaban Tottenham wajen daukar dan wasan Inter Milan mai tsaron bayan tawagar Slovakia, Milan Skriniar, mai shekara 27. (Football Insider)   

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp na duba yiwuwar katse wasannin aro da dan kwallon Brazil, mai shekara 26 Arthur Melo ke yi a Juventus domin ya kai dauki Anfield (Mirror)

Real Madrid da Chelsea sun bi sawun Liverpool da Manchester United wajen rige-rigen cinikin dan kwallon tawagar Ingila, Jude Bellingham, mai shekara19, daga Borussia Dortmund a kaka mai zuwa. (Sport - in Spanish)

Liverpool za ta mayar da hankali kan daukar dan wasan Wolves sabon dan kwallon tawagar Portugal, Matheus Nunes, mai shekara 24, idan ta kasa sayen Bellingham. (UOL, via Mail)

Paris St-Germain na son kyaftin din Argentina, Lionel Messi, mai shekara 35, da mai tsaron bayan Sifaniya, Sergio Ramos, mai shekara 36, su sabunta kwantiraginsu a kungiyar. (AS - in Spanish)

Mai tsaron bayan Turkiya, Caglar Soyuncu, mai shekara 26, zai bar Leicester City zuwa Atletico Madrid idan yarjejeniyarsa ta kare a King Power a karshen kakar bana. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Kociyan Roma, Jose Mourinho na son daukar aron tsohon dan wasan tawagar Ingila ta matasa ‘yan kasa da shekara 21, Trevoh Chalobah, mai shekara 23, daga Chelsea in January. (Sport - in Spanish)

Everton ta fara tattaunawa da Anthony Gordon, mai shekara 21, kan damka masa sabon kwantiragi mai tsoka wadda zai kai linki shida kan albashin da yake karba a yanzu. (Independent)

Watakila dan wasan Brazil, Allan, mai shekara 31, da na Venezuela Salomon Rondon, mai shekara 33, su bar Everton bayan da wasu kungiyoyi daga Hadaddiyar Daular Laraba ke son zawarcin ‘yan wasan. (90min)

Wolves ta ci gaba da tattaunawa da mai tsekara 27, mai tsaron bayan Belgium, Jason Denayer, wanda bai da kungiyar, bayan barin Lyon a kakar da ta wuce. (Teamtalk)

Chelsea ta taya dan wasan AC Milan dan kasar Portugal, Rafael Leao, mai shekara 23, tun kan fara kakar bana. (Fabrizio Romano)

Ana daf da sanar da nada tsohon kociyan Shakhtar Donetsk, Roberto de Zerbi, mai shekara 43, a matakin mai horar da Brighton, wadda za ta bai wa dan kasar Italiya yarjejeniya zuwa karshen kakar 2024 da cewar za a iya tsawaitata idan ya taka rawar gani. (Nicolo Schira)