Real Madrid ta lashe Uefa Super Cup kofin farko a kakar bana

An wallafa

Real Madrid ta lashe Uefa Super Cup na 2022/23, bayan da ta doke Eintracht Frankfurt da ci 2-0 a ranar Laraba a Hensinki a Finland.

Real ta fara cin kwallo ta hannun David Alaba saura minti takwas su je hutu, haka kuma suka yi kungiyar Sifaniya tana da ci 1-0.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Karim Benzema ya kara na biyu da ya bai wa Real lashe kofin farko a kakar bana.

Ana buga Uefa Super Cup, don tunkarar kakar tamaula ta Zakarun Turai ta gaba, inda ake wasan tsakanin wadda ta ci Champions League da wadda ta lashe Europa League a gasar da ta wuce.

Real Madrid ce ta lashe Champions League a kakar da aka kammala, bayan da ta doke Liverpool a Faransa, ita kuwa Frankfurt nasara ta yi a kan Rangers a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1.

Ranar Juma'a za a fara kakar La Liga ta bana, inda Real Madrid za ta ziyarci UD Almeria.

A kakar da ta wuce Real Madrid ta dauki Sifanish Super Cup da La Liga da kuma Champions League.

Haka kuma a bara Karim Benzema ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga da kuma Champions League.

Real Madrid wadda ta lashe Uefa Super Cup na bana, na sa ran daukar Sifanish Super Cup da Copa del Rey da La Liga da Champions League da kuma World Clubs Cup.