Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fellaini ya sanar da yin ritaya daga taka leda
Tsohon dan wasan Everton da Manchester United, Marouane Fellaini ya sanar da yin ritaya.
Mai shekara 36, wanda ya buga wa tawagar Belgium wasa 87 da zuwa gasar kofin duniya karo biyu ya bar yi wa kasarsa tamaula a 2019.
Fellaini ya koma Everton daga Standard Liege a 2008 daga nan ya je Manchester United a 2013, sai kuma kungiyar da ke buga gasar China, Shandong Luneng a 2019.
Fellaini ya buga wa Belgium wasan Olympics a 2008 da Euro 2016 da zuwa gasar cin kofin duniya a 2014 da kuma 2018.
Ya yi karawa 141 a Premier League a Everton da cin kwallo 25 da bayar da 14 aka zura a raga.
Fellaini ya zura kwallo 22 a raga a karawa 177 a dukkan fafatawa a United, wanda ya lashe FA Cup a 2016 da Europa League da EFL Cup a 2017 a kungiyar ta Old Trafford.