Waiwaye: Kashe 'yan Najeriya 1,715 cikin wata uku da wa'adin da aka bai wa maniyyata don biyan kuɗin Hajji

An wallafa

Abubuwa da dama sun faru a makon da ya gabata a Najeriya, ciki har da mutanen da sojoji suka ceto daga 'yan bindiga a jihar Kebbi da kuma wa'adin da hukumar kula da aikin Hajji ta bai wa maniyyata don biyan kuɗin kujera.

Wannan maƙala na ɗauke da wasu muhimmai daga cikin abubuwan da suka faru.

Ƴan bindiga sun kashe mutum 1,715 a Najeriya cikin wata uku

Wani rahoto na kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a Najeriya ya ce ƴan bindiga sun hallaka mutum 1,715 a faɗin Najeriya tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2023.

A cikin rahoton wanda kamfanin ya fitar yau Alhamis, ya ce an kashe mutane mafi yawa ne a yankin arewa maso gabashin ƙasar, inda aka kashe mutum 491.

Sai kuma yankin arewa masotsakiyar ƙasar inda aka kashe mutum 366.

Arewa maso yammacin ƙasar ne na uku a yawna mutanen da aka kashe, inda aka kashe mutum 362.

Jihohin da lamarin ya fi muni su ne Borno da Filato da kuma Zamfara.

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro a yankunan daban-daban na ƙasar, waɗanda suka haɗa da na ƴan fashin daji a arewa maso gabas da Noko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.

Bugu da ƙari ana fama da matsalar ƴan fashi da kuma masu garkuwa da mutane a arewa maso tsakiya da kuma kudancin ƙasar.

Tashin farashin gas na girki na ƙara damun magidanta a Najeriya

Ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa game da yadda farashin gas ɗin girki ya yi tashin gwauron-zabi a baya-bayan nan.

A wasu wurare a jihar Kano ana sayar da kilo ɗaya na gas din kan naira 1,000 wasu kuma 1,100.

Wannan na zuwa ne yayin da bayanai ke cewa abubuwa da dama ne suka haddasa tsadar gas din ciki har da karancinsa.

Bayanan da BBC ta samu na cewa farashin gas din na ci gaba da tashi a sassan Najeriya.

Tukunyar gas ɗin girki mai nauyin kilo 12 a yanzu ana sayar da ita a kan 12,000, a wasu wuraren kuma fiye da haka.

Wani mai sayen gas a Kano, Sanusi Mannir Garba ya shaida wa BBC cewa" yanzu na zo sayen kilo 12 kuma na saye shi a kan 10,900, saɓanin a baya da muke saye kan 8900."

Karanta cikakkiyar maƙalar a nan:

An bai wa maniyyatan Najeriya wa'adin mako uku su biya miliyan 4.5 kuɗin ajiya

Hukumar Alhazan Najeriya ta bai wa maniyyata aikin hajjin bana wa'adin makonni uku da su biya naira miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiyarsu.

Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne kasancewar makonni uku ne kawai suka rage mata na kammala daidaitawa da masu tafiyar da lamuran aikin Hajji a Saudiyya.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa - hannun mataimakiyar daraktan hulda da jama'a na hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta ce hukumomin saudiyya sun sanya ranar 4 ga watan Nuwamba domin kammala duk wata tattaunawa da masu kula da lamuran aikin hajji na ƙasar.

Kan haka ne hukumar ke buƙatar samun ƙiyasin maniyyatan aikin hajin bana domin samun damar ƙayyade farashin aikin hajjin banan.

Sanda Usara ta ce fara shirye-shiryen aikin hajin 2024 da wuri ya sa hukumar Alhazan ƙasar da na jihohin ƙayyade kudin ajiya na naira miliyan 4.5

Sojoji sun ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su a jihar Kebbi

Dakarun Operation Hadarin Daji, a ranar Alhamis, sun ce sun yi nasarar ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su tare da karɓe babura daga hannun ƴan bindiga a yayin wani aikin ceto a jihar Kebbi.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Kyaftin Yahaya Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce an samu nasarar hakan ne a lokacin da sojojin da aka jibge a Malekachi suka gudanar da aikin ceto sakamakon sahihan bayanai da ke nuna cewa ‘yan bindaga sun yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a kauyen Kanya da ke karamar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi inda suke ƙoƙarin tsallakawa da su zuwa Nijar.

Sanarwar ya ce “Sojoji sun yi kwanton bauna a kan hanyoyin da ake zargin ‘yan ta’addan ne za su yi amfani da su a kauyen Karenbana..

Bayan haka, karfin wuta na sojojin ya tilastawa 'yan ta'addan suka tsere da raunukan harbin bindiga tare da barin waɗanda suka yi garkuwa da su wanda ya kai ga ceton su.

“Wadanda aka ceto sun hada da mata 6 da maza 11 da suka hada da ‘yan sanda da aka yi garkuwa da su a Danko-Wasagu."

"An mika waɗanda aka ceto ga jami’an ‘yan sanda na yankin Bena domin sada su da iyalansu. Haka kuma, sojojin sun kwato Babura 5 da suka kone,” in ji sanarwar.

Ya kuma ƙara da cewa kwamandan rundunar hadin gwiwa, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya yabawa matakin da sojojin suka mayar a kan lokaci, inda ya buƙace su da su ƙara kaimi tare da ci gaba da hana ‘yan ta’addan ‘yancin kai dauki.

Me dawo da canjin dala ga masu shiga da shinkafa Najeriya yake nufi?

Babban Bankin Najeriya CBN ya ɗage haramcin bayar da chanjin dala don shigar da shinkafa da wasu kayyaki 42 cikin ƙasar a wani yunƙuri na tallafa wa kasuwar musayar kuɗi na 'lokaci zuwa lokaci'.

A shekarar 2015 ne CBN ya taƙaita bayar da dala domin shigar da wasu abubuwa ƙasar, yana mai cewa bai su kamata a bayar da dala domin shigar da su ba, kasancewar ana iya samar da su a cikin ƙasar.

To sai dai cikin wata sanarwar da CBN din ya fitar ranar Alhamis, mai ɗauke da sa hannun babban daraktan sadarwa na CBN ɗin, Isa AbdulMumin, ya ce kayyakin da ɗage wa haramcin ya shafa sun haɗar da shinkafa da sumunti da man ja da nama da kaji da sabulu da kayan kwalliya da sauran abubuwa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a yanzu masu shigo da abubuwa 43 za su iya samun chanjin dala daga babban bankin na CBN.

To ko me hakan yake nufi ga noman shinkafa a ƙasar?

Karanta malabƙalar da muka rubuta kan hakan a nan:

An ɗaura auren zawarawa da ƴan mata a Kano

Dangi da ƴan'uwa gami da abokan arziƙi ne suka halarci Babban Masallacin Juma'a na Kano, inda suka shaida auren zawarawa da ƴan mata da gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyin gudanarwa.

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta nauyin auren zawarawa da 'yan mata kimanin 1,800 don tallafa musu wajen gina tushen rayuwar iyali da kyautata harkokin zamantakewa.

An daura auren ne a Babban Masallacin Juma'a na Kano da kuma a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Shugaban hukumar na HISBA Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yace sun kafa wani kwamiti da zai rika bibiyar amaren don tabbatar da cewa sun zauna lafiya kuma babu saki ko cin mutunci.

Sannan ya ce za su samar da kotun tafi-da-gidanka don gurfanar da duk angon da ya ci zarafin amaryarsa.

Ga wasu daga cikin hotunan angwayen a lokacin da suka halarci wurin daurin aure na Babban Masallacin Juma'ar.

Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar EFCC

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Ngelale ya bayyana cewa naɗin Olukoyede, na tsawon shekara hudu ne a matakin farko, amma sai majalisar dattawa ta tabbatar da shi.

Sanarwar ta ce shugabancin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na ƙasar na samun sauye-sauye cikin 'yan watannin da suka gabata, tun bayan hawan Bola Tinubu karagar mulki a ranar 29 ga Mayu.

A ranar 14 ga watan Yunin 2023, Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC, kuma har yanzu yana tsare a hannun hukumomi ba tare da an gurfanar da shi gaban shari'a ba.

Sanarwar ta ce Tinubu ya dakatar da Bawa ne "don ba da damar yin ingantaccen bincike kan yadda ya gudanar da aiki lokacin shugabancinsa".

Matakin ya zo ne bayan zarge-zarge ''masu nauyi'' na tozarta mukaminsa, in ji sanarwar.

Daga nan ne shugaban ya umurci daraktan ayyuka na hukumar Abdulkarim Chukkol ya rike shugabanci EFCC a mataki na wucin gadi.