Firmino zai tafi Juventus, Ronaldo na kokarin tserewa daga United

Asalin hoton, Getty Images
Bayanai na cewa dan wasan gaba na Liverpool kuma dan asalin kasar Brazil Roberto Firmino na gab da komawa kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke wasa a kasar Italiya. (Corriere dello Sport - In Italian)
Idan hakan ta faru, da alama ke nan Juventus za ta dakatar da kokarinta na dauko dan wasan gaba na Chelsea Timo Werner, mai shekara 26, da kuma dan wasan Manchester United Anthony Martial. (Corriere dello Sport - In Italian)
Manchester City a yanzu tana da zabin dauko dan wasan baya na Sifaniya Alex Grimaldo, mai shekara 26, wanda Benfica ta yanka masa farashin Yuro miliyan 20. (Marca - In Spanish)
Bournemouth ta cimma yarjejeniyar dauko dan wasan tsakiya na Ingila, mai taka leda a Middlesbrough, Marcus Tavernier kan kudi fam miliyan 15. (90min)
Nottingham Forest na nuna sha’awar dauko dan wasan tsakiya na Real Betis, William Carvalho. (Mail)
Barcelona na gab da shan gaban Chelsea wajen sayen dan wasan baya Jules Kounde, mai shekara 23, bayan cimma yarjejeniya da Sevilla kan farashinsa yuro miliyan 50. (Guardian)
Batun tafiyar Nuno Tavares a matsayin aro daga Arsenal zuwa Atalanta na rawa, bayan da Atlanta din ta ki amincewa da bukatar Gunners na mika shi kai-tsaye tare da zabin sayen dan wasan dan asalin Portugal mai shekara 22. (Michele Criscitiello, via football.london)
Har yanzu Manchester United na sa ran za ta iya dauko dan wasan tsakiya na Barcelona dan asalin kasar Netherlands Frenkie de Jong. (Give Me Sport)
De Jong dai ya shaida wa abokan wasansa na Barca cewar ba shi da niyyar barin Nou Camp a wannan kakar duk da nacin da United ke nunawa na daukar sa. (Cadena Ser, via Mirror)
Cristiano Ronaldo ya shaida wa Manchester United cewa yana bukatar a sakar masa mara ya nemi wata kungiya da za ta buga gasar zakarun Turai (Champions League).
Sai dai United ta nanata cewar ba ta son sayar da dan wasan dan asalin kasar Portugal mai shekara 37. (Daily Mail)
Paris St Germain ta yi fargar-jaji wurin taya dan wasan gaba na Italiya Gianluca Scamacca, mai shekara 23, jim kadan kafin kammala yarjejeniyar komawar sa West Ham daga kungiyar kwallon kafa ta Sassuolo. (Sky Sports)
Dan wasan gaba na Uruguay Luis Suarez, mai shekara 35, ya sanya hannu kan kwantaragin komawa kungiyar kwallon kafa ta Nacional. (Fabrizio Romano)









