Trump ya kudiri aniyar kawo karshen yaƙin Ukraine bayan tattaunawa da Putin

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Donald Trump ya ce yana shirin ganawa ido da ido da Vladimir Putin, wanda zai kawo karshen shekarun da aka kwashe Amurka na nisantar shugaban na Rasha.

Ya ce ganawarsu ta farko za ta kasance a Saudiyya.

Sanawar na zuwa ne sa'o'i bayan Mista Trump ya yi tattaunawar tsawon mintuna casa'in ta wayar tarho da Mista Putin, ya kuma ce, sun amince su yi aiki tare domin kawo karshen yakin Ukraine.

Mista Trump ya kuma fadawa 'yan jarida cewa baya ganin akwai dacewa Ukraine ta shiga Nato.

"Tun kafin shugaba Putin, suna cewa babu ta yadda zasu amince da hakan. Wannan yanayi ne da aka kwashe shekaru masu yawa ana fama. Suna ta fadin hakan a tsawon lokaci, cewa Ukraine ba zata iya shiga Nato ba, kuma bani da damuwa da hakan.

"Ina son fadin kalma guda...Ko da abu ne mai kyau ko akasin hakan. Amma tabbas kamar yadda galibin mutane ke cewa ne, abu ne da ba zai yiwu ba."

Fadar Kremlin dai ta nuna cewa ita ma ta yarda cewa lokaci ya yi na aiki tare da Trump.

Daga bisani kuma Donald Trump ya kira Shugaba Volodymyr Zelensky.

A lokacin tattaunawa da 'yan jarida, Mista Zelensky ya zayyana abubuwan da suka tattaunawa, sannan ya ce babu wani abu na boye-boye.

"Ina godewa shugaban saboda gaskiyar da ya fito fili ya nuna mana, da kuma yadda zamu yi aiki tare domin cimma zaman lafiya.

"Magana ce mai tsawo da ta danganci diflomasiya da tsaro da tattalin arziki. Shugaba Trump ya kuma fadamun abin da Putin ya fada mai.

"Mun yarda da karfin Amurka, tare kuma da kokarinmu da abokan huldarmu, hakan ya isa matsin lamba ga Rasha da tilastawa Putin zaman lafiya."

Trump dai ya tattauna batutuwa da dama da shugabannin biyu da suka danganci Gabas ta Tsakiya da Kirkirarriyar Basira ta AI, da kuma hanyoyin kawo karshen yaƙin Ukraine.

Sannan Trump ya umarci sakataren harkokin wajensa da shugaban hukumar tsaro ta CIA da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro su jagoranci tattaunawar sulhu da Rasha, wanda shugaban Ukraine ya ce shima an sanar da shi.