'Yan wasan Amurka sun sha kalaman wariya bayan rashin nasara a Copa America

An wallafa

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Amurka ta yi tir da kalaman wariya da aka dinga yi wa 'yan wasan tawagarta bayan doke ta 2-1 a wasan da suka buga da Panama a gasar Copa America da take karɓar baƙunci.

Ma'abota shafukan sada zumunta sun yi ta faɗa wa 'yan wasa Folarin Balogun na Monaco da kuma abokan wasa a Juventus Tomothy Waeh da Weston McKennie maganganu.

An buga wasan na Rukunin C a birnin Atalanta, inda aka bai wa Weah mai shekara 24 jan kati bayan ya naushi ɗan wasan Panama Roderick Miller.

Sai dai ɗan wasan ya nemi afuwar abokan wasansa yana mai cewa "ɓacin rai ne ya jawo".

Hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar US Soccer ta faɗa cikin wata sanarwa cewa: "Ba za a taɓa lamuntar irin waɗannan kalaman na tsana da wariya ba.

"Wannan ba abin yin tir ba ne kawai, ya kuma saɓa wa al'adarmu ta girma ma juna da jan kowa a jiki da aka san mu da ita."

Amurka ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Balogun - ƙwallonsa ta biyar kenan cikin wasa 14 - kafin Cesar Blackman ya farke wa Panama minti huɗu tsakani.

Amurkar ta ci gaba da tsare gida amma zuwa minti na 83 Jose Fajardo ya ci ta biyu, amma kuma ita Panama ta ƙare da mutum 10 a cikin fili bayan korar Adalberto Carrasquilla daga wasan.

Sakamakon ya sa mai masaukin baƙin ta koma ta biyu a teburi da maki uku iri ɗaya da Panama, abin da ke nufin dole ne ta samu aƙalla irin sakamakon da Panaman za ta samu a wasan ƙarshe na rukunin kafin ta iya wuce zagayen kwata fayinals.