Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da ƙyar idan zan sake wasa karkashin Amorim - Rashford
Marcus Rashford na jin ba zai sake taka leda a Manchester United ba karkashin Ruben Amorim.
Sai dai ɗan wasan tawagar Ingila ya ce ba zai yi gaggawar yanke hukunci kan makomarsa ba.
Rashford ya ci ƙwallo huɗu tun bayan da ya koma buga wasannin aro a Aston Villa daga watan Fabrairu, har da wacce ya ci City ranar Talata da suka yi rashin nasara.
Manchester City ta doke Aston Villa a Etihad 2-1 a wasan Premier League, inda ƙungiyar Etihad ta koma ta ukun teburi, bayan wasan mako na 34.
Ƙwantiragin Rashford zai kare a karshen kakar bana a Aston Villa.
Sai dai yarjejeniyar ɗan ƙwallon a United za ta karkare a karshen kakar 2028, kenan zai sake komawa Old Trafford da zarar wa'adinsa ya kare a Villa Park.
Tun cikin watan Disamba Amorim ya ajiye Rashford, bayan wasa da Newcastle United ranar 30 ga watan Disamba, wanda ya shiga karawar daga baya.
Kenan United tana da zaɓin ko dai ta sayar da matashin mai shekara 27 ko kuma ta kara bayar da aronsa ga wata ƙungiyar.
Wata majiya daga Rashford ta ce ɗan wasan bai tattauna da mahukuntan United ba kan makomarsa, wanda yake son a tayar da batun a tsakiyar watan Yuni
Haka kuma Rashford baya son batun yin musaya da shi da Eberechi Eze zuwa Crystal Palace, kamar yadda aka daɗe ana ta raɗe-raɗin batun.
Rashford ya ci ƙwallo huɗu a wasa 17 a Aston Villa da bayar da shida aka zura a raga.