Babu shaidar USAID ce ke ɗaukar nauyin Boko Haram - Jakadan Amurka

Richard Mills

Asalin hoton, Richard Mills/X

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills ya musanta zarge-zargen da ke nuna cewa hukumar USAID ce ke bai wa ƙungiyar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta'adda kuɗaɗen gudanarwa.

Mista Mills wanda ya bayyana hakan yayin wata gana wa da ƙungiyar gwamnonin Najeriya a Abuja da daren Laraba, ya ce babu wata hujjar da ke nuna hakan.

Ya kuma ƙara da cewa babu wata ƙasa a duniya ta yi alawadai da Boko Haram kamar Amurka, inda ya ba su tabbacin cewa idan an samu shaida, gwamnatin ta Amurka za ta yi aiki tare da gwamnatin najeriya wajen binciken batun.

"Kwata-kwata babu hujjar dangane da wannan zargi, idan kuma da mun samu hujjar cewa akwai wani shirin da Boko Haram ke amfana daga shi, ba tare da ɓata lokaci ba za mu binciki al'amari bisa haɗin gwiwar abokan hulɗarmu na Najeriya." In ji Mills.

"Muna aiki tare da hukumomin Najeriya a lokutan bincike. Ina ba ku tabbacin cewa muna da tsare-tsare mai tsauri wajen tabbatar da cewa kuɗaɗen tallafi daga USAID koma daga kowane irin tallafi daga Amurka ko USAID ko hukumar tsaro ko ma'iakatar ƙasashen waje, ba a karkatar da su ba ga ƙungiyoyin ta'adda kamar Boko Haram.

Saboda haka idan ana maganar Boko Haram, Amurka na tare da Najeriya wajen yaƙar ƙungiyar ta Boko Haram da aƙidunta.

"Bari na yi muku gwari-gwari— Babu wata ƙawar Najeriya da ta yi alawadai da Boko haram kamar Amurka. Mun ayyana Boko Haram a matsayin ƙungiyar ta'adda tun 2013, inda muka hana ƙungiyar safarar kuɗaɗe zuwa Amurka da kuma samun damar kama ƴan ƙungiyar." In ji Mills.

A ranar 13 ga watan fabrairu ne dai wani ɗan majalisar Amurka, Scott Perry ya zargi USAID da tallafa wa ƙungiyoyin ta'addanci da suka haɗa da Boko Haram.

Perry, wanda ɗan jam'iyyar Republican ne daga Pennsylvania, ya yi iƙrarin ne lokacin wani zaman sauraro da ƙaramin kwamitin majalsiar kan ayyukan gwamnati da ingancinsu ya yi.

Zaman mai taken "Yaƙi da almubazzarancie: Kawo ƙarshen kashe kuɗaɗen ta hanyar da ba su dace ba da almundahana," ya yi duba ne kan yadda ake kashe kuɗaɗn masu haraji na Amurka.

Perry ya ce tallafin USAID kai tsaye ya amfani ƙungiyoyin ta'adda a duniya kamar Boko Haram da Al-Qaeda da ISIS.

Ya yi zargin cewa kasafin USAID na shekara ya kai dala miliyan 697da suka haɗa kuɗaɗen da ake bai wa makarantun Islamiyya da suka zama silar samar da sansanin horas da masu tsaurin ra'ayi da ƙungiyoyin ta'adda.

Majalisar dattawa ta gayyaci hukumomi da hafsoshin tsaro

Sanata Mohammed Ali Ndume

Asalin hoton, Ndume

A zamanta na ranar Laraba, majalisar dattawan Najeriya ta gayyaci mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da darekta janar na hukumar leken asirin Najeriya, NIA Mohammed Mohammed da hafsoshin tsaro na Najeriya domin bayar da bahasi kan zarge-zargen da ake yi wa USAID.

Shugaban majalisar ta dattawan, Godswill Akpabio wanda ya sanar da gayyatar a lokacin zaman ya ce mutanen da aka gayyata ɗin za su bayyana ne a gaban ƴan majalisar a wani zama na sirri domin jin bahasinsu.

Wannan dai ya biyo bayan buƙatar da sanata mai wakiltar jihar Borno, Ali Ndume ya nema dangane da binciken.

Sanata Ndume dai ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da irin barazanar da ƙungiyar ta Boko Haram ke yi ga rayuwar al'ummominsu duk da irin kuɗaɗen da gwamnatin Najeriya ke kashewa a yaƙi da ita.

Ya nemi majalisar ta binciki gaskiyar zargin da aka yi wa hukumar USAID dangane da tallafa wa ƙungiyar Boko Haram.