Arsenal ta koma ta daya a teburin Premier League

An wallafa

Arsenal ta koma matakinta ta daya a teburin Premier League, bayan da ta doke Brentford 3-0 ranar Lahadi a wasan mako na takwas.

Gunners ta fara cin kwallo minti na 17 ta hannun William Saliba, minti 11 tsakani Gabriel Jesus' ya kara na biyu, sannan Fabio Vieira ya ci na uku.

Hakan ya sa Arsenal ta hada maki 18 da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City da Tottenham masu maki iri daya.

Ranar Asabar Manchester City ta hau kan teburin Premier, bayan da ta ci Wolves 3-0 a Molineux.

Ita kuwa casa Tottenham casa Leicester City ta yi da ci 6-2 a dai ranar ta Asabar.

Ranar 1 ga watan Oktoba Arsenal za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan hamayya a gasar Premier a Emirates.

Wasan da suka buga a kakar da ta gabata

2021/2022

Premier League Asabar 19 ga watan Fabrairun 2022   

  • Arsenal            2 - 1     Brentford       

Premier League Friday 13 ga watan Agustan 2021    

  • Brentford        2 - 0     Arsenal

Wasu batutuwa kafin Karawa a tsakaninsu ranar Lahadi

Brentford ta yi nasara a wasa biyar daga shida da ta karbi bakuncin Arsenal, koda yake sauran haduwar a cikin shekara 1930 suka fafata, in banda a bara da Brentford ta ci 2-0 a gida.

Wasan da Gunners ta ci a gidan Brentford shi ne 1-0 a Mayun 1947.

Brentford

  • Wasa daya aka doke Brentford daga 17 baya a gida a karawar hamayya ta kungiyoyin birnin Landan, shi ne wanda Chelsea ta ci 1-0 cikin Oktoban 2021, Brentford ta yi nasara a 13 da canjaras uku.
  • Kungiyar ta zura kwallo hudu daga wajen da'ira ta 18 a bana, wadda a gabaki dayan kakar bara uku ta ci a 2021/22.
  • Kungiyar da Thomas Frank ke jan ragama ta ci kwallo 15 a kakar nan, Manchester City ce kan gaba a wannan kwazon.
  • Yoane Wissa ya zura kwallo biyar a matakin dan wasan canji a bana, ba wanda ya kai shi bajintar nan.

Arsenal

  • Arsenal ta yi nasara a biyar daga takwas bayan nan da ta fuskanci kungiyoyin Landan a fafatawa 23.
  • Watakila ta lashe wasan hamayyya na uku a jere da kungiyar birnin Landan a karon farko tun Maris din 2015.
  • Arsenal ta yi wasa 23 ba tare da yin canjaras ba ko dai ta ci ko a doke ta, wadda ta yi nasara a 16 da shan kashi a bakwai daga ciki.
  • Kowacce kwallo 10 baya da Arsenal ta ci an zura ne da kafar hagu.
  • Kafin fara wasannin karshen mako, Gabriel Jesus ne kan gaba a taba kwallo 66 a da'irar abokiyar karawa, mai yanka 34 da aka yi wa keta sau 21.