Zan sakar wa kananan hukumomi mara a Bauchi - Sanata Jika

Bayanan bidiyo, Zan mayar da hankali kan fansho da sakar wa kananan hukumomi mara a Bauchi -Sanata Jika
Zan sakar wa kananan hukumomi mara a Bauchi - Sanata Jika
An wallafa

A ci gaba da kawo muku ‘yan takarar kujerar gwamna a jihohin Najeriya, a yau za kawo muku Sanata Halliru Dauda Jika mai takarar neman gwamnan jihar Bauchi a jam’iyyar NNPP.

A hirarsa da Halima Umar Saleh, Sanata Halliru Jika ya ce zai mayar da hankali kan fadada kudaden shiga da inganta rayuwar matasa da kuma ‘yan fansho.

Ya kara da cewa zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ya sakar wa kananan hukumomi mara domin rage radadin talauci.