An dakatar da Reece James da kuma cin sa tarar fam 90,000

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An dakatar da kyaftin din Chelsea, Reece James daga buga wasa daya tare da cin sa tarar kuɗi fam 90,000.

Lamarin ya faru ne bayan da Aston Villa ta ci Chelsea 1-0 a cikin Satumba, wanda ya tayar da hatsaniya lokacin da ƴan wasa ke komawa dakin sauya kaya.

Mai tsaron bayan ya yi kalamai na cin zarafi da baƙaƙen maganganu da kuma nuna rashin ɗa'a ga alkalan wasan.

Tun farko an bayar da rahoton cewar dan kwallon tawagar Ingila ya kalubalanci alkalin wasa Jarred Gillett.

Mai shekara 23 bai fafata ba a karawar, sakamakon jinya da yake yi.

James ya ji raunin ne a lokacin atisaye a watan jiya a raunin da ya yi ta fama da shi tun daga kakar 2022-23.

Chelsea ta karasa wasan da ta buga da Villa da 'yan kwallo 10 a cikin fili ranar 24 ga watan Satumba, inda Ollie Watkins ne ya zura dayar a raga.

An bai wa mai tsaron bayan tawagar Faransa, Malo Gusto jan kati a minti na 58, bayan ƙeta mai muni da ya yi, yayin da mai kula da VAR, ya bukaci Gillett ya duba lamarin sosai

Tun farko an bai wa Gusto katin gargadi kan ketar da ya yi wa mai tsaron bayan Villa, Lucas Digne daga baya Gillet ya ba shi jan kati, bayan da ya je ya kalli abin da ya faru..

Chelsea tana mataki na 11 a teburin Premier League, wadda ta ci wasa biyu daga bakwai da ta kara kawo yanzu a kakar nan karkashin Mauricio Pochettino.