Majalisun dokoki sun amince da kasafin kuɗin Najeriya na naira tiriliyan 54.99

Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin ne a watan Disamba

Asalin hoton, NASS

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Majalisun dokokin Najeriya sun amince da ƙudirin kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2025 na naira tiriliyan 54.99, a zamansu na ranar Alhamis.

Kasafin wanda ke ƙunshe da kuɗaɗen yau da kullum da manyan ayyuka da biyan bashi da kuma hasashen samun kuɗin da za a cike giɓin kasafin kuɗin kamar haka:

  • Kasafi hukumomi da ma'aikatu: Naira tiriliyan 3.65
  • Kuɗaɗen gudanarwar gwamnati: Naira tiriliyan 13.64
  • Kuɗaɗen manyan ayyuka: Naira tiriliyan 23.96
  • Kuɗaɗen biyan bashi: Naira tiriliyan 14.32
  • Giɓin da ke cikin kasafi: Naira tiriliyan 13.08

A ranar 5 ga watan Fabrairu ne shugaba Tinubu ya ƙara yawan kuɗin kasafin na 2025 daga naira tirirliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, bisa dalilan samun ƙarin yawan kuɗaɗen shiga da hukumomi suka samar wa gwamnati.

Tinubu ya nemi majalisun su amince da ƙarin yawan kasafin a wasiƙu da ya aike wa majalisun guda biyu da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta.

Shugaba Tinubu ya ce ƙarin ya samo asali ne bayan samun ƙarin kuɗin shiga na naira tiriliyan 1.4 da huukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS ta yi da kuma naira tiriliyan 1.2 da hukumar Kwastam ta samar sai kuma naira tiriliyan 1.8 da sauran hukumomin gwamnati suka bayar.

A watan Disamban 2024 ne dai shugaba Bola Tinubu ya yi miƙa kasafin ga majalisun dokokin ƙasar da ya yi wa suna da "Farfaɗowa: Tabbatar da Zaman Lafiya, da Gina Rayuwa".

Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 47.9, wanda yana shekarar da ta gabata da kashi 36.8 cikin 100. Shi ne na biyu da Tinubu ya yi tun bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023.

An dai ɗora kasafin kuɗin na 2025 na Najeriya ne a kan dala 75 a kan kowacce gangar ɗanyen mai guda kuma ana sa ran Najeriyar za ta samar da gangar ɗanyen man fiye da miliyan biyu duk rana a shekarar mai kamawa.

Shugaba Bola Tinubu ya shaida wa majalisun dokokin cewa "muna fatan samun naira tiriliyan 34.82 ta hanyar kuɗin shiga domin zuba wa a kasafin".

Sai dai kuma ya ce kasafin na da giɓin naira tiriliyan 13.08 wato kashi 3.08 cikin 100 na jimillar kasafin, yayin da ake hasashen gwamnatin za ta ciyo bashin tiriliyan 13 a cikin gida da waje domin cike giɓin.