Hotunan yadda fari ke bankaɗo ɓoyayyun taskokin ƙarƙashin ruwa

An wallafa

Nahiyar Turai na fuskantar makonni na fari, matsalar da matsanancin zafi ya haifar da kwashe mutane har ma da rasa rayukan al'umma.

Wasu koguna da tafkuna sun kafe, lamarin da ya zama matsala ga jiragen ruwa masu amfani da hanyoyin ruwan domin jigilar kaya da fasinoji.

Sai dai janyewar ruwan ta bayyana wasu albarkatu da a baya suke boye a karkashin ruwa.

Mafi daure kai sune duwatsun da aka lakaba wa suna "duwatsun yunwa", wadanda aka zana a gabar wasu koguna a shekarun baya a matsayin kashedi ga al'umomi ma su zuwa cewa da zarra sun ga duwatsun sun bayyana, to akwai yunwa da tarin matsaloli da ke tafe.

Yawancin duwatsun sun sake bayyana a gabar kogin Elbe, wanda ruwansa ya taso daga Jamhuriyar Czech ya bi ta cikin ƙasar Jamus.

Daya daga cikin duwatsun, wanda tun karni na 15 aka yi masa wannan alamar, ya bayyana a shekarar 1616, lokacin mazauna yankin suka karta wani sako mai cewa "idan aka ganni, a fashe da kuka".

Rashin isasshen ruwa a kogin Danube a cikin kasar Serbia ya bayyana wasu jiragen yaki biyu daga lokacin da aka gwabza Yakin Duniya na Biyu, wadanda aka tarar da su dauke da bama-baman da ba su fashe ba.

Wadannan jiragen yakin biyu, wadanda aka gano su kusa da garin Prahovo, na cikin wata tawagar jiragen yakin sojojin Nazi na Jamus da aka nutsar da su a 1944.

Ana sa rn wasu jiragen za su bayyana yayin da ruwan ke kara kafewa.

An kuma gani wasu bama-baman da ba su fashe ba a cikin kogin Po da ke kasar Italiya.

Kimanin mutum 3,000 aka kwashe daga wani kauye da ke kusa da birnin mantua a watan Yulin, yayin da kwararru suka ciro wani bam na zamanin Yakin Duniya na Biyu a cikin kogin kuma suka tarwatsa shi ba tare da ya raunata kowa ba.

Akwai kuma wani karamin jirgin ruwa da sojojin Jamus suka yi amfani da shi wanda janyewar ruwan Kogin na Po ya bayyanar da shi, wanda a shekarar 1943 aka nutsar da shi.

Mazauna yankin dai sun fara ganin saman jirgin ruwan mai suna Zibello ya bayyana yayin da ruwan kogin ya fara kafewa ciki watannin da suka gabata, sannan daga baya sai kara bayyana yake yi sannu a hankali yayin da wannan yanayi na fari ke karuwa.

Karancin ruwa a Kogin Tiber a birnin Rum na Italiya ya bayyana wata tsohuwar rusassiyar gada wadda ake tunanin Sarki Nero na tsohuwar daular Rum ya gina a shekara ta 50 miladiyya.

Dama a kan rika ganin saman rusasshiyar gadar a shekarun baya a duk lokacin da ruwa ya ɗan janye, amma ba kamar yanzu ba da ake iya ganinta sosai.

Tsohuwar gadar na karkashin wata sabuwar gadar da aka gina ne mai suna Vittorio Emanuele II.

A Sifaniya kuwa, wasu jerin duwatsu da ake kira "Spanish Stonehenge" sun bayyana a cikin madatsar ruwa ta Valdecanas da ke yankin Caceres na tsakiyar kasar.

A hukumance ana kiransu duwatsun "Dolmen na Guadalperal", kuma ana hasashen wannan jerin duwatsun tun shekaru 5,000 kafin bayyanar annabi Isa suke wannan wurin.

Wani mai binciken tarihi ne ya fara gano su a 1926, sai dai a wancan lokacin ruwa ya mamaye yankin saboda wata madatsa da aka gina domin raya yankin a 1963.

Tun wancan lokacin, sau hudu kawai aka taba ganinsu.

A Galicia da ke kan iyakar Portugal, wani kauye ya bayyana a farkon wannan shekarar saboda fari ya sa ruwan wata madatsar ruwa ya bushe baki dayansa.

An tara ruwa a kauyen Aceredo ne a 1992 domin samar da madatsar ruwa a wurin.

Wasu daga cikin mazauna wurin sun koma domin kallon gidajen nasu da a yanzu suka ruguje.

Wasu albarkarun da suka bace a karkashin ruwa a Birtaniya ma sun bayyana.

An gano wani rusasshen gini na wani tsohon coci a kauyen Derwent na yankin Derbyshire.

A 1940 ne dai aka tara ruwa a yankin domin samar da madatsar ruwa ta Ladybower.

An kuma ga ragowar wasu tsofaffin bishiyoyi a madatsar ruwa ta Colliford da ke Cornwall na kasar Birtaniya.

A shekarun 1980 ne dai aka tara ruwa a wannan wurin mai suna Bodmin Moor.

Sannan akwai alamun wani wurin shakatawa wanda aka taba shuka furanni a Lydiard Park na Swindon, da ke yankin kudu maso yammacin Ingila, bayan da ruwa mai zafi ya kashe ciyawar da ke wurin kuma ya bayyana ainihin kasar da ke wurin.

An kuma ga irin wadannan batattun wuraren shakatawar a Longleat, cikin wani babban gida da ke kusa.