Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana binciken Chelsea kan cininkin Eto'o da Willian
Cinikin da Chelsea ta yi kan Samuel Eto'o da Willian a shekarar 2013 ya faɗo cikin wani ɓangare a binciken da Premier League ke yi kan yuwuwar keta ka'idojin cinikayya.
Masu ƙungiyar ta Chelsea sun ce "Cinikayyar da aka yi a lokacin ya faru ne kafin zuwan waɗanda ke mallakan ƙungiyar a yanzu" kuma "ba su da alaƙa da duk wani mutum da ke ƙungiyar a halin yanzu".
Hukumar Uefa ta ci tarar Chelsea fam miliyan 8.6 a watan Yuli saboda karya ƙa'idojin hada-hadar 'yan wasa wato Financial Fair Play, sakamakon "rashin ba da cikakkun bayanan kuɗi" tsakanin 2012 da 2019.
Sabbin masu hannun jari a kungiyar ne suka bayar da rahoton, bayan sayar da ƙungiyar a watan Mayun 2022, kuma an fahimci cewa sun sanar da hukumar Premier League a wannan lokacin.
An tabbatar da binciken a cikin watan Agusta, kuma kamar yadda jaridar Times ta ruwaito, ana duba batun sayen ɗan wasan Kamaru Eto'o da ɗan wasan tsakiya na Brazil Willian.
Dukkan 'yan wasan biyu sun koma ƙungiyar ne a ƙarƙashin mallakar Roman Abramovich, wanda ke riƙe da kungiyar daga 2003 zuwa 2022.
Dukkansu sun ƙulla yarjejeniya ne daga ƙungiyar Anzhi Makhachkala ta ƙasar Rasha.
Abramovich ya sayar da ƙungiyar Chelsea ga wata ƙungiyar haɗin gwiwa ƙarƙashin jagorancin mai saka hannun jari na Amurka Todd Boehly da kuma kamfanin Clearlake Capital mai zaman kansa a bara.