Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashen Yamma za su fara kwashe 'yan ƙasashensu daga Nijar
Faransa da Italiya sun ce sun shirya kwashe 'yan ƙasashensu da sauran Turawa mazauna Nijar daga ranar Talatar nan, kwana shida bayan juyin mulkin da ya kifar da ɗaya daga cikin shugabanni masu ƙawance da Ƙasashen Yamma, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Faransa ce ta fara bayyana shirin kwashe 'yan ƙasarta daga Nijar, kafin Italiya ta sanar da irin wannan niyya, bayan kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed.
Sawun farko na Faransawa mazauna Nijar za su fara barin ƙasar ne da yammacin Talata, a cewar ministar harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna.
Ta ce ɗaruruwan Faransa ne mazauna Niamey da sauran biranen Nijar ne za a kwashe ta jirgin sama zuwa gida.
Ta ce ta ɗauki matakin ne saboda wani mummunan hari da masu zanga-zanga suka kai wa ofishin jakadancinta ranar Lahadi da kuma ganin an rufe sararin samaniyar Nijar, don haka 'yan ƙasarta ba su da 'yancin fita ta hanyar amfani da jiragen saman fasinja.
Ita ma, ma'aikatar harkokin wajen Jamus a ranar Talata ta shawarci Jamusawa mazauna Niamey babban birnin Nijar, ƙasar da sojoji suka yi juyin mulki, su karɓi tayin ficewa daga ƙasar a jiragen kwasar 'yan ƙasashen waje na Faransa.
"Abokan ƙawancenmu na Faransa sun gabatar da tayi, kuma cikin 'yan kujerun da ake da su, don kwashe Jamusawa daga Nijar, " cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen.
"Ma'aikatar harkokin waje ta ba shawarar... dukkan Jamusawa da ke Niamey su karɓi wannan tayi." Ma'aikatar ta yi imani cewa akwai aƙalla Jamusawa fararen hula 100 da ke zaune a Nijar.
Matakin na zuwa ne bayan shugabannin mulkin soji a maƙwabtan ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Guinea sun bayyana goyon bayansu ga sabbin mahukuntan Nijar.
Sojoji masu juyin mulki sun ƙwaci iko a cikin ƙasashen Afirka ta Yamma huɗu tun daga shekara ta 2020.
Tuni dai ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar ɗaukar "dukkan matakai" idan ba a mayar da Shugaba Bazoum kan karagar mulki ba.
Ita dai tsohuwar uwargijiyar Nijar wato Faransa ta ce tsaron rayukan al'ummar ƙasarta, muhimmin abu ne da take bai wa fifiko.
Faransa na da dakarun soji 1,500 a yanki, waɗanda ke taimakon ƙasashen Sahel wajen yaƙi da 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi.
Ministar harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna ta faɗa a ranar Litinin cewa zanga-zangar da aka yi a gaban ofishin jakadancin ƙasarta da kuma zarge-zargen cewa dakarun tsaron Faransa sun yi harbi cikin taron mutane, in ji ta duk ba gaskiya ba ne.
Juyin mulki a Nijar ya ƙara tsoron da ake da shi game da sha'anin tsaro a yankin Sahel.
Shugabannin mulkin soji a Burkina Faso da Mali sun ce duk wnai yunƙuri na mayar da Shugaba Bazoum kan mulki da ƙarfi, za a ɗauke shi a matsayin wata shelar yaƙi.
Ana tsare da hamɓararren shugaban Nijar ɗin ne a Niamey, babban birnin ƙasar.
Maƙwabtan ƙasashe sun rufe iyakokinsu da Nijar
A wani ɓangare kuma, rahotanni na cewa ƙasashe maƙwabtan Nijar kamar Benin da Najeriya duk sun rufe kan iyakokinsu da ƙasar bayan takunkuman da ƙungiyar raya ƙasashen Afirka ta Yamma ta sanya wa ƙasar.
Benin dai tana da iyaka kai nisan kilomita 1,060 da Jamhuriyar Nijar, inda ta raja'a da Benin ɗin wajen safarar kayayyaki daga ciki ko zuwa wajen ƙasar ta Tekun Atlantika.
Bayanai sun ce an dakatar da manyan motoci ɗauke da kayayyaki zuwa Nijar a kan iyakokin ƙasashen biyu.
Haka zalika, rahotanni daga Nijar sun ce Najeriya ma ga alama ta ɗauki makamancin wannan mataki na rufe kan iyakarta da Nijar, don kuwa harkoki a bakin iyakar ƙasashen biyu sun tsaya cik.
Iyakar Najeriya da Nijar na da tsawon kilomita 1,608 daga yammaci daura da Jamhuriyar Benin har zuwa gabashi inda ta kai iyaka da Chadi.